Connect with us

RAHOTANNI

Akasarin Masu Zuwa Asibitin Kunne Na Kaduna Na Da Alamomin COVID-19

Published

on

Shugaban Asibitin Kunne na kasa dake a Kaduna Dakta  Mustpha Abubakar dan Yaro ya sanar da cewa, Asibitin ya dauki kwaraan matakai akan annobar COVID-19 ganin cewar, asibitin shine yafi damumwa, idan akayi la’kari da  mafi yawancin marasa lafiyar dake  zuwa Asbitin suna zuwa ne da larurar yin tari da kuma atishawa wadanda kuma, irin wadannan   sune alamomin cutar ta COVID-19.

Dakta  Mustpha Abubakar dan Yaro wanda ya sanar da hakan a hirarsa da manema labarai a jiya Laraba ya ci gaba da cewa, yana da wuya a gane ko marasa lafiyar da yazo asibitin yana dauke da cutar ta COVID-19.
Ya ce, a saboda haka ne, Asibitin ya dauki kwararan matakan da suka kamata don baiwa ma’aikatan sa da kuma marsa lafiyar dake zuwa Asibitin tare da rage yawan masu zuwa asibitin don a duba lafiyar in dai ba zuwan na gaggawa bane.
Ya ci gaba da cewa, Asibitin ya kuma tanadi kayan aiki  don kare ma’aikatan sa da kuma marasa lafiya masu zuwa a duba su don kada marasa lafiyar su harbi ma’aikatan ko kuma ma’aikatan su harbi marasa lafiyar, inda kuma hakan zai janyo yada ta a cikin alummar gari.
Dakta Mustapha Abubakar dan Yaro ya kuma yi kira ga daukacin yan Nijeriya dasu kiyaye wajen bin matakan da ma’aikatar kiwon lafiya ta tarayya ta dauka ta kuma sanar da jama’a don gudun kada su harbu da cutar, inds ya kara da cewa, wasu daga cikin kariyar ta hada da, rage yin zirga-zirga in bata gaggawa bace, wanke hannuwa, dsina yawan kusanta da juna, inda ya yi nuni da cewa, ta hakan ne kawai za’a iya yakar annobar.
A karshe, Dakta Abubakar dan Yaro ya sanar da lambobin wayar tafi da gidanka da alumma zasu iya tuntubar Asibitin   don bayar da shawara kamar haka: 07084665308, 08023729068.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: