Connect with us

LABARAI

Ba A Amince Da Amfani Da ‘Chloroquine’ A Matsayin Maganin Koronabairus -NCDC

Published

on

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Nijeriya wato NCDC, ta yi gargadi cewa ba a amince a rika amfani da maganin Chloroquine ba wajen magance cutar Koronabairus (COVID-19).

Dr Chikwe Ihekweazu, Darakta Janar na NCDC, shi ne ya yi wannan gargadin a Abuja a ranar Alhamis, a yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da wasu kafafen watsa labarai ke yadawa cewa ana iya amfani da maganin ‘chloroquine’ wajen kare kai daga cutar COVID-19 ko warkar da mutanen da suke fama da cutarCOVID-19.

“Ya kamata ‘yan Nijeriya su fahimci cewa amfani da chloroquine da ire-iren maganin, hukumar lafiya ta duniya, WHO ba ta amince da maganin ba wajen magance cutar COVID-19.

“Akwai dai fata daga masu bincike, sai dai har yanzu ba a amince da maganin wajen warkar da cutar COVID-19 ba.” inji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: