Connect with us

RAHOTANNI

COVID-19: Gwamnatin Bauchi Ta Umarci Ma’aikata Su Rika Aiki Daga Gida

Published

on

Gwamnatin jihar Bauchi ta umurci dukkanin ma’aikatan jihar da suke matakin aiki na 1 zuwa 12 da su ci gaba da gudanar da aiyukansu daga cikin gidajensu domin kiyaye kai daga cutar COVID-19.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da jami’an watsa labarai na shugaban ma’aikatan jihar, Umar Sa’idu ya fitar a jiya, ya shaida cewar an dauki matakin ne domin kariya daga cutar numfashi mai hanzarin kisa ta Coronabirus.
A cewar sanarwar a bisa bazuwar da cutar ta yi a sassan kasashen duniya wanda a Nijeriya mutum 42 suka kamu, ta dauki matakan dakile yaduwar cutar da kuma kiyaye ma’aikatan jihar.
Umar Saidu ya ce, ma’aikatan da suke kan aiki na musamman ne kawai za su ci gaba da zuwa ofisoshinsu domin ci gaba da gudanar da aiki tare da ma’aikatan da suke aiki daga mataki na 13 zuwa sama, inda su gwamnati ta nemi su ci gaba da zuwa aiki domin tabbatar da aiki na gudana yanda aka tsara.
A cewar sanarwar ta shugaban ma’aikatan jihar; “A kokarin da ake yi na kiyaye yaduwar cutar, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya umurci dukkanin wadanda basu aiki na musamman wadanda suke matakin aiki daga 1 zuwa 12 da suke yin aiki daga gida daga yau Laraba 25 Maris, 2020.
“Dukkanin ma’aikata da suke matakin aiki na 13 zuwa sama tare da masu aiki na musamman da irin su ma’aikatan lafiya, jami’an tsaro da su ci gaba da fitowa bakin aiki da gudanar da aiki domin tabbatar da aiki na tafiya yanda ya dace,” A cewar jami’an watsa labaran.
Sanarwar ta kara da cewa, ta nemi ma’aikatan jihar da su ci gaba da rungumar matakan kariya domin kiyayewa daga cutar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: