Connect with us

RAHOTANNI

COVID-19: Gwamnatin Kogi Ta Killace Mutum Bakwai

Published

on

A kokarin da takeyi na dakile cutar Covid-19,wanda akafi sani da Corona birus, gwamnatin jihar Kogi ta killace mutum bakwai  tare da sanya idanu akansu har na tsawon makwanni biyu.

Kwamishinan kula da kiwon lafiya na jihar, Dakta Saka Hakuna Audu ne ya bayyana hakan a yayin da yake yiwa manema labaru karin haske a ranan talatar data gabata akan ci gaban da gwamnatin jihar ta samu wajen yaki da cutar na Corona birus a jihar.
Yayi bayanin cewa kawo yanzu babu rehotun kes din bullar cutar na COVID 19 a jihar, inda ya kara da cewa mutum bakwai da aka killace sunyi  balaguro ne cikin wata guda zuwa kasashen da cutar ke da hadarin gaske,lamarin da acewarsa ya zama wajibi a killace su,yana mai cewa rigakafi yafi magani. Dakta Audu yace mutum biyar daga cikin wadanda aka killacen sun fito ne daga karamar hukumar Lokoja,a yayin da kuma biyu suka fito daga kananan hukumomin Ajaokuta da Okene.
A karshe kwamiahinan yace gwamnatin jihar ta Kogi na daukar dukkan matakan da suka kamata wajen ganin cutar ta Corona birus bata yadu ba a fadin jihar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: