Connect with us

MANYAN LABARAI

Covid-19: kalau Na Ke Tamkar dan Dambe – Martanin Gwamnan Kogi Ga PDP

Published

on

  • Ka Mika Kanka A Gwada Ka, Cewar PDP
  • An ki Wayon, In Ji Shi

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya mayar da martani zazzafa ga babbar jam’iyyar adawa a jihar tasa dangane da kiran da ta yi ma sa na ya mika kai bori ya hau ta hanyar zuwa a yi ma sa gwajin annobar cutar nan ta Covid-19, inda Gwamna Yahaya ya ce, lafiyar kalau tamkar dan dambe.

A ’yan kwanakin nan dai an yi ta yada rahotannin cewa, gwamnan na Jihar ta Kogi ya kamu da muguwar cutar bayan da wasu jiga-jigan Nijeriya su ka ziyarce shi, don yi ma sa ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa, Marigayiya Hajiya Hawa’u Ozuohu Bello, a garin Okene kwanakin baya.
Cikin wadanda su ka ziyarce shi din akwai Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Tarayya, Malam Abba Kyari, wanda a yanzu haka a ka tabbatar da cewa, ya na fama da cutar bayan an yi ma sa gwaji a farkon makon nan.
Wannan dalilin ya sanya PDP fitowa ta shawarci gwamnan da cewa, lokaci ya yi da zai gaggauta mika wuya, domin a binciki lafiyar tasa.
Jam’iyyar ta PDP, a wata sanarwa da daraktanta na bincike da adana bayanai a jihar, Achadu Dickson, ya sanya wa hannu, ta ce, yaki da cutar ta Covid-19 zai samu nasara ne kawai idan dukkan masu ruwa da tsaki su ka nuna lallai da gaske su ke yi, sannan ta bukaci dukkan wadanda su ka yi mu’ammala da kuma musabaha da Babban Hadimin Shugaban kasar Abba Kyari da su kai kawunansu a yi mu su gwaji, don amfanin lafiyarsu da kuma na sauran al’umma.
Sanarwar kazalika ta roki jam’iyyar APC mai mulkin jihar da kas da kada ta sanya siyasa a harkokin lafiya da kuma rayukan al’ummar jihar ta Kogi, amma duk da hakan sai PDP din ta yi addu’a da kuma fatan cewa a karshe za a gano Gwamna Bello ba shi dauke da cutar.
Sai dai kuma Jam’iyyar PDP, har ila yau, ta ce, ita dai har yanzu ba ta ga wani shiri da gwamnatin jJihar Kogi ta ke yi ba na yaki da cutar a jihar idan banda rufe makarantu da kasuwanni da tashoshin motoci da kuma hana tarurukan jama’a ba.
A kan haka nema jam ‘iyyar ta PDP mai hamayya ta yi Kira ga gwamnatin jihar da ta yi koyi da jihohin Barno da Legas da kuma sauran jihohi, inda su ka nuna jajircewarsu da kuma kudurinsu na yaki da cutar.
Jam’iyyar adawar ta kara da cewa, abin takaici ne a ce gwamnatin jihar ta Kogi ta na yi wa cutar da ta buwayi duniya rikon sakainar kashi. Sai kuma jam’iyyar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta yi wa jama’a sassauci a dokar da ta kafa ta hana taro, wanda a cewarta, hakan na neman wuce gona da iri ta hanyar tauye wa jama’ar jihar hakkinsu.
To, amma a wani gajeran faifan bidiyo da Gwamna Belllo ya saki a jiya Laraba, ya hakikance cewa ko kadan ba shi dauke da cutar, inda ya ce, duk wanda ya yi ma sa fatan kamuwa da cutar Covid-19, shi kuma ya yi mi shi fatan kamuwa da cutar nan ta karya garkuwar jiki, wato HIV.
Kamar yadda ya ce, “idan ka na tababar matsayin lafiyata, to Ina kalubalantar ka da ka zo mu fafata a gasar damben, mu ga wanda zai yi nasara.”
A ranar Talatar da ta gabata ne dai a ka gano Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammed, ya na dauke da cutar bayan an gwada shi, inda ya kasance gwamna na farko a Tarayyar Nijeriya da ya kamu da cutar, wacce ta fara zama ruwan dare a tsakanin manya a duniya bakidaya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: