Connect with us

RAHOTANNI

COVID-19: Ku Dafa Wa Gwamnati – Gwamnan Gombe Ga Sarakuna

Published

on

A jiya Talata ne gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya gana da Sarakuna da Hakimai, inda a yayin ganawar ya shawarci sarakuna da su karfafi kokarin gwamnatin jihar na dakile yaduwar cutar Coronabirus domin kare lafiya da rayukan jama’an jihar.

A shawarar da ya basu lokacin da ke ganawa da masu girma Sarakunan jihar, ya kara da cewa kiran ya zama dole lura da kokarin da suke yi na kare lafiya da rayukan kowani dan jihar da tabbatar da cutar nan ta Corona ba ta shigo jihar ba sam-sam.
Ya ce a bisa yaduwar da cutar take yi a tsakanin jama’a a sassan duniya, akwai bukatar masu ruwa da tsaki su tashi domin bayar da tasu gudunmawar wajen yaki da cutar a tsakanin jama’a.
Inuwa ya ce, al’umma tana cikin wani lokaci mafi hadari wanda ya ce dole ne a lalubo hanyoyin da suka dace domin kare kawuka da lafiyar jama’a daga cutar.
Gwamna Yahaya ya ce a kokarin da gwamnati ta yi kawo yanzu har da kafa kwamiti na musamman mai mutum 21 da aka daura wa alhaki sanya ido don tabbatar da jihar ta wanku daga annobar cutar ta Corona.
Daga bisani gwamnan ya bukaci masu rike da mukaman siyasa da suke jihar da su hada kai da sarakuna domin kara wayar da kan al’ummominsu domin kariya daga cutar, wanda a cewarsa ta hanyar wayar da kai da fadakarwa za a samu nasarori sosai wajen kyautata kiwon lafiyan jama’a da rigakafi daga annobar.
Shugaban kwamitin sanya ido kan cutar Corona a jihar Gombe, Farfesa Idris Muhammad, ya shawarci Sarakuna da Hakiman da su dauki gangamin wayar da kan jama’an da suke mulka domin duk a hadu tare a kuma tsira tare daga cutar ta Corona.
A jawabinsa Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu-Abubakar III, a maidadin dukkanin sarakunan jihar, ya sha alwashin mara wa gwamnatin jihar baya domin cimma wannan nasarar da ta sanya a gaba na kyautata lafiyar jama’an jihar musamman ta kokarin dakile yaduwar Corona.
Shehu-Abubakar, ya kuma gode wa kokarin gwamnatin jihar na kare rayuka da dukiyar jama’an jihar, sai ya tabbatar da cewar za su bayar da tasu gudunmawar domin kiyaye jihar daga cutar.
Wakilinmu a Gombe ya shaido mana cewar a yayin ganawar an yi zama a tsakanin mutum da mutum ta hanyar bayar da tazara da wara-wara domin kiyayewa daga cutar ta Corona.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: