Connect with us

RAHOTANNI

COVID-19: Majalisar Dokokin Gombe Ta Dakatar Da Harkokinta Makonni Uku

Published

on

Majalisar Dokokin jihar Gombe da ta dakatar da dukkanin harkokin da suka shafi majalisar na tsawon sati uku domin kiyayewa daga cutar Coronabairus mai hanzarin kisan jama’a.

Shugaban majalisar jihar, Alhaji Abubakar Sadik Ibrahim, shine ya sanar da batun dakatar da harkokin majalisar tare da umurtar dukkanin ma’aikatan majalisar da su zauna a gidajensu daga jiya Laraba 25 ga watan Maris zuwa ranar 14 ga watan Afrilun 2020.
Hon. Sadik Ibrahim ya sanar da hakan ne ta cikin kwafin sanarwar manema labaru da babban jami’in watsa labarai na majalisar Abubakar Umar ya fitar tare da rabar wa ‘yan jarida a Gombe jiya.
Kakakin ya kuma shaida cewar wannan matakin ya kuma shafi ma’aikatan da suke aiki a karkashin hukumar majalisar dokokin jihar.
A cewar shi; daukar matakin dakatar da harkokin majalisar na daga cikin yunkurin ‘yan majalisar na mara wa kokarin gwamnan jihar Inuwa Yahaya baya na dakile yaduwar cutar da rigakafin kamuwa da ita.
A fadin Kakakin, jagorancin majalisar ya maida hankali kan walwala da jin dadin hadi da kula da rayuka da lafiyar ma’aikatansu tare da illahirin al’umman jihar don haka akwai bukatar su dauki matakan da suka dace domin dafa wa gwamnatin na rigakafin cutar.
Sanarwar ta Kakakin majalisar ta kuma bukaci al’umman jihar da su bi dukkanin matakan da gwamnatin ta dauka domin kariya kan daga cutar tare da bin shawarorin likitoci domin tabbatar da cutar ba ta barke a jihar ba.
Kakakin daga bisani sai ya nemi ‘yan jaridu da su ke bai wa jama’a labaran da suka dace kuma sahihai domin tabbatar da cutar dai ba ta samu wurin zama a jihar ba da kuma kiyaye ruda hankulan jama’a.
Daga bisani sai ya gargadi ‘yan social media masu yada labaran da basu da inganci musamman kan batutuwan da suka shafi cutar domin tabbatar da komai a mizaninsa.
Daga bisani sai ya jinjina wa kokarin gwamnatin na daukan matakan da suka dace don kiyaye al’umman jihar daga cutar tare da daukar matakin wayar da kan jama’a muhimmancin kula da kansu don kariya daga cutar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: