Connect with us

RIGAR 'YANCI

COVID-19: Sakataren Gwamnatin Gombe Ya Bukaci Jagororin Kisirtoci Su Yi Addu’a

Published

on

Sakataren gwamnatin jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya bukaci shugabannin addinai a jihar da su ci gaba da yin addu’o’i na musamman domin kare Nijeriya daga annobar Coronabirus.

Farfesa Njodi, wanda ke bayanin hakan a jiya lokacin da ke jawabi ga shugabannin cocin ECWA reshen Kaltungo, ya kara da cewa, a matsayinsu na bayin Allah muminai, akwai bukatar su kara jan damara da zage damtse wajen yi wa jihar Gombe da kasa hadi ma da duniya addu’a na musamman domin kawo karshen cutar numfashi mai hanzarin kisa ta Corona da ta addabi duniya a halin yanzu.
Sakataren gwamnatin jihar ya roki shugabannin addinan da a kowani lokaci suke yin abubuwan da za su tabbatar da hada kan ‘yan kasa a maimakon yin abubuwan da za su jawo rabuwan kawuka a fadin kasa, wanda yake cewa, nuna banbancin addini bashi da wani fa’ida ga jama’a.
Daga bisani ya gode wa jagororin reshen cocin ECWA na Kaltungo da suka kawo masa ziyara na musamman domin taya shi murnar samun mukamin SSG, yana mai ce musu wannan zabi ne daga Allah da kuma kokarin da gwamnan jihar Mohammed Inuwa Yahaya ke yi wajen jawo wadanda suka dace domin kyautata aiki.
Tun da farko, shugaban reshen Cocin ECWA a Kaltungo, Rabaran Gerson Laushigi ya ce sun halarta a ofishin SSG din ne domin taya shi murnar samun mukamin da yayi biyo bayan nadin da gwamnan jihar ya masa, sai suka gode wa gwamna Inuwa Yahaya a bisa zabin da yayi tare da nuna godiyar al’ummar Kaltungo gareshi bisa karamcinsa a garesu.
Ya kuma ce, sun zo ofishin domin yin addu’a na musamman don samun nasarar dakile yaduwar cutar nan ta Coronabirus da tabbatar da cutar ba ta barke a jihar ba kwata-kwata.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: