Connect with us

LABARAI

Ganduje Na Ci Gaba Da Daukar Matakan Dakile Yaduwar Cutar Koronabairus A Kano

Published

on

A ci gaba da kokarin da gwamnonin jihohi ke yi domin ganin sun dakile yaduwar cutar Koronabairus a Nijeriya, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na ci gaba da daukar matakan dakile yaduwar cutar a jiharsa, duk da dai har yanzu dai babu wani wanda ya kamu da cutar daga jihar.

A wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya sanyawa hannu, ya bayyana cewa; daga ranar Juma’a 27 ga Watan Maris din nan, da karfe 12 na dare ne za a rufe duk hanyoyin shigowa jihar Kano. “Duk cikin kokarin ko-ta-kwana na gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje saboda neman tsari daga mummunar cutar nan ta Koronabairus.” inji sanarwar.

Haka nan sanarwa ta kara da cewa dukkan fasinjoji masu zuwa jihar ta bangaren zirga-zirga na cikin gida, ta filin jirgin saman Malam Aminu Kano, ba za a bar su shiga cikin garin Kanon ba, sai dai su zauna a filin jirgin saman.

Sannann za a yi amfani da hukumomin ‘yan sanda da na KAROTA da na Hisbah da sauransu domin za su sa ido sosai wajen ganin an yi aiki da wannan umarni.

Sannan an umarci jama’a da su bai wa jami’ain hadin kai. Sannan kuma har wala yau an nemi  jama’a da su bi shawarwarin jami’an lafiya.

Har wala yau gwamnnan ya nemi da ma’aikatan gwamnati ka da  su je Ofis; “An yi hakan ne domin su zauna a gidajensu saboda tsare kansu. Haka nan dukkan jama’a a na shawartarsu da kan janye jikinsu daga kasuwanni, in dai ba bisa abinda ya zama dolen dole ba.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: