Connect with us

LABARAI

Jihohin Da Masu Cutar Koronabairus A Nijeriya Suke

Published

on

A ci gaba da bankado wadanda suka kamu da cutar Koronabairus a Nijeriya da Cibiyar dakile cututtuka ta Nijeriya, NCDC ke wallafawa a shafinta na Twitter, ya zuwa 11:25 na daren Larabar 25 ga watan Maris din 2020, an tabbatar da cewa mutane biyar sun sake kamuwa da cutar wanda adadinsu yanzu ya kai 51. 

Sabbin adadin da suka kamu da cutar sun fito ne daga Abuja inda akwai guda biyu, sai Legas guda 2 sai kuma guda daya daga Ribas wadanda duka sun dawo Nijeriya ne daga kasar waje, yayin da guda biyu daga cikinsu sun yi muámala da masu cutar ne.

Ya zuwa yanzu dai mutum daya ne kawai ya rasa ransa daga cutar, yayin da aka sallami mutum biyu.

Ga Jihohin da wadanda suka kamu da cutar suka fito:

Legas- 32
Abuja- 10
Ogun- 3
Ekiti- 1
Oyo- 1
Edo- 1
Bauchi-1
Osun-1
Rivers-1
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: