Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Kaunar kur’ani Ya Sa Mu Karrama Attajiri Sambajo – Gwani Turaki

Published

on

An bayyana tsananin kaunar Alkur’ani da son Ahlullahi na shahararren dan Kasuwar nan, Alhaji Salisu Sambajo a matsayin dalilin da yasa Majalisar Mahaddata Alkur’ani ta kasa, karkashin Shugabancin Gwani Aliyu Salihu Turaki Babban Limamin Masallacin Alhassan dantata da ke Jihar Kano, ta karrama wannan bawan Allah. Shugaban Majalisar Mahaddatan na kasa ne ya bayyana haka a Kano, ranar Litinin da ta gabata lokacin da suka ziyarce shi (Alhaji Salisu Sambajo) a Ofishinsa.

Gwani Turaki, ya bayyana kyawawan halayen Alhaji Salisu Sambajo a matsayin wanda ya gada daga wurin mahaifinsa, musamman ta fuskar hidinmatawa Alkur’ani da kuma Ahullahi. Ya kara da cewa, na san shi kyakkywan sani, kuma abubuwan da yake yiwa Alkur’ani ko shakka babu abin a gode masa ne kuma jama’a ya kamata su yi koyi da ire-iren ayyukan alhairinsa. Sannan a kuma yi duba da irin kyawawan shawarwarin da yake baiwa wannan tsari da fadakar da ‘yan’uwa, gaskiyar al’marin yadda za a kara inganta tsarin karatun tsangaryunmu yasa dole ‘yan’uwa ke kara jinjinawa kokarin na Sambajo.
Don haka, sai ya bayyanawa Sambajon cewa, bayan doguwar tattaunawa a matakin Shugabancin Majalisar ta kasa, mun yanke shawarar baiwa Alhaji Salisu Sambajo wannan lambar karramawa, sannan kuma Mahaddata Alkur’ani sun amince da nadin Alhaji Salisu Sambajo, a matsayin Garkuwan Mahaaddata Alkur’ani na kasa, wanda idan Allah Ya kai mu taronta na kasa a wannan shekara, za a gudanar da nadin nasa a gaban mai Alfarma Sarkin Musulmi da yardar Allah, “ in ji Turaki.
Shi ma da yake gabatar da nasa jawabin, Sakataren Majalisar Mahaddatan na kasa Goni Sanusi Abubakar, ya tunawa ‘yan’uwa Mahaddata irin gagarumar gudunmawar da Alhaji Salisu Sambajo ke baiwa harkokin addini da kuma hidimtawa Alkur’ani. Haka kuma, ya bayyana farin cikinsa bisa samun irin wadannan bayin Allah, wadanda yanzu suka yi karanci a cikin al’umma.
Goni Sunusi, ya nuna gamsuwar ‘yan’uwa tare mika sakon Mahaddata fatan Sambajo zai kara rubanya kokarinsa wajen abinda yake yi na hidimtawa Alkur’ani da al’umma baki-daya. A karshe kuma ya yi addu’ar fatan Allah Ya kara wa Jihar Kano zaman lafiya ya kuma yayewa al’umma matsalolin da ke addabarsu a wannan lokaci.
Da ya ke gabatar da nasa jawabin, Alhaji Salisu Sambajo Shugaban Rukunin Kamfanoni Sambajo Enterprises, ya godewa Allah bisa samun wannan karramawa, ya ce, na samu lambobin yabo masu yawa ciki har da wadda Shugaban kasa ya ba shi, amma bai taba jin dadin samun karramawar da ta kai wannan wadda Alhalullahi suka yi masa ba. “Zan jima ina godiya tare da tuna wannan karramawa da aka yi min.”
Alhaji Salisu Sambajo, ya koka kwarai bisa rashin hadin kan da ke damun al’ummar Hausa/Fulani, wanda ya ce mu kadai ne muka rasa jagoranci. A fadin nasa, duk fadin Arewa babu wanda ke da kimar da zai ce a yi ko bari, a kuma hannu a kan abinda ya ambata. Daga nan ne, sai ya bayar da misali da harkokin kasuwanci musamman a Jihar Kano, inda ya ce matukar batun kasuwancin ake a Kano dole a sallamawa Alhaji Aminu dantata, amma ko shi idan da a ce zai fito ya tsawatar kan wani al’amari da ke bukatar gyara a harkokin kasuwancin, kashegari za ka ji an baiwa wani dan Dako kudi ya shiga rediyo ya yi ma sa tatas.
Haka nan wannan lamari yake ta fuskar Malamai, Sarakuna da ‘yan siyasa, ba mu da wani jagora da muka amince da shi wajen tsawatarwa ko kuma bayar da wani umarni, domin magana da murya guda. Don haka sai ya bukaci wannan Majalisa ta Mahaddata Alkur’ani da su yi kokarin sanya Allah a cikin dukkanin al’amuransu, wannan ita ce hanya daya tilo mai bullewa.
“Sai an kaucewa munafunci da tsogali tsoma, an yarda da Shugabanci tare da yin biyayya ga Shugabanni. Hakan ne zai taimake mu wajen samun cikakken hadin kai da kuma cigaban da mu ke fata,” in ji shi.
A karshe, ya nuna farin cikinsa tare da yin alkawarin cigaba da wannan kyakkyawan zato da aka yi ma sa. “Ni tunda na taso haka na ga Mahaifina na yi wa harkokin Alkur’ani hidima tun muna Alagbodo, kullum mahaifinmu cikin hidimtawa Alkur’ani yake, mu gidanmu baya rabuwa da Almajirai wanda ake gudanar da karatun alkur’ani koda-yaushe.
Saboda haka, sai ya bukaci Mahaddatan su kara jajircewa wajen yi wa Jihar Kano da kasa baki-daya addu’a tare da rokon Allah Ya magance mana wannan annoba da ta kunno kai a halin yanzu. Daga nan, sai ya yi addu’ar fatan Allah Ya mayar da kowa gidansa lafiya.
Cikin kunshin tawagar da ta ziyarci Garkuwan Mahaddatan na kasa, akwai Shugaban Majalisar Mahadatan na kasa, Gwani Aliyu Salihu Turaki, Sakatarenta na kasa Goni Sunusi Abubakar, Sakataren Majalisar reshen Jihar Jigawa, Gwani Nasiru Jigawa, Gwani Bashir dan Mahiru, Gwani Hammdu M. Uzairu, Kwamared Zakariyya, Malam Nazifi Abubakar, Malam Rabiu Tarauni da sauransu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: