Connect with us

NOMA

Noman Kwakwar Manja Zai kara Samarwa Da Nijeriya Kudaden Shiga

Published

on

Noman Kwakwar Manja zai kara bunkasa samarwa da kasar nan kudaden shiga masu yawa.

A cewarsu, umarnin Gwamnatin Tarayya na watknnin baya kan harkame iyakokin Nijeriya na kan tudu, ya taimaka matuka masu sarrafa Manja a kasar nan harda masu yin amfani dashi.
Henry Olatujoye wanda Injiya ne kuma shugaban kwamitin amintattu na kungiyar maau sarrafa Manja ta kasa PPAN ya sanar da cewa, koda yake a lokacin mulkin Obasanjo da Jonathan, sunyi kokari wajen fargado da fannin, musamman a bangaren shuka Kwakwar Manja.
Ya cigaba da cewa daukin kwanan baya da babban bankin Nijeriya CBN a fannin da kuma kokarin da ya yi na daukaka fannin an samar da chnaji mai dorewa.
A cewarsa, idan a ka kwatanta Kwakwar Manja da sauran a fannin na Kwakwar Manja anfi samu riba.
Henry Olatujoye wanda Injiya ne kuma shugaban kwamitin amintattu na kungiyar maau sarrafa Manja ta kasa PPAN, fannin na daya dake kan gaba wajen samar da ayyukan yi akan kadada 1,000, unda kuma zai samar da ayyukan yi kai tsaye ga ma’aikata su 200, inda ya kara da cewa, shuka Kwakwar Manja, zai kara samar da ayyukan yi in har gwamnati ta samar da tsari mai kyau, musamman don samar da ayyukan yi ga matasan dake kasar nan.
A cewar Henry Olatujoye wanda Injiya ne kuma shugaban kwamitin amintattu na kungiyar maau sarrafa Manja ta kasa PPAN, manyan kasashen da suka kasance suna a kan gaba wajen sarrafa Manja tsari ne da gwamnati ta kikiro dashi ga kasashe suka samar da Irin noman Kwakwar Manja da kuma kula da nomanta.
Ya ce, misalai, bazaka mallaki kadadar noma data kai yawan 10,000 a kasar Malaysiya ba, sanna kace wai kana sarra Manja ba, hakan ba zai yiwu ba domin zasu baka lasisi don ka kafa inda ake sarrafa Manjan.
Olatujoye wanda uma shine Babban Jami’I a Kamfanin Palmfield Debelopment Processing, ya yi nuni da cewa, idan gwamnati ta zuba kudade maau yawa a fannin mai makon bayar da dauki, hakan ba zai yiwa manomi wani alfanu ba.
Henry Olatujoye wanda Injiya ne kuma shugaban kwamitin amintattu na kungiyar maau sarrafa Manja ta kasa PPAN, ya kima bayar da shawarar kan hanyoyin da gwamnati ya kamata tabi don kara bunkasa fannin wadanda sulanhada da, samar da tsarin da ya dace a daukacin jihohin da su ke da ra’ayon noman Kwakwar Manja.
Ya ce, sole ne gwamnati ta kasance a shirye wajen samar da isashen Irin na Kwakwar Manja, inda Henry Olatujoye wanda Injiya ne kuma shugaban kwamitin amintattu na kungiyar maau sarrafa Manja ta kasa PPAN ya kara da cewa, akwai bukatar yawan sanya ido akan malaman gona don a tabbatar da cewa, dukkan Irin Kwakwar Manja da gwamnati ta samar an shuka su yadda ya dace.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: