Connect with us

NOMA

Yadda Covid-19 Ta Shafi Hada-hadar Fitar Da Amfanin Gona Waje

Published

on

Manyan kasashe masu karfin tattalin arziki sun kasa yin wani katabusa saboda annobar Cutar coronavirus.

kwararru sun sanar da cewa, masu fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje zasu iya sanun kawunan su a cikin yanayin matsalar fitar da amfani zuwa kasashen wajen.
Duk da kokarin da kasashen suke yi da suka kamu da annobar cutar ta coronavirus wajen yaduwar ta akan hada-hadar kasuwanci a fadin duniya.
Masu yin fashin baki da dama sun bayyana cewa, kwayar cutar, ta dakile ci gaban tattalin arzikin duniya.
Sashen hada-hadar kasuwanci da samar da ci gabk na Majalisar dinkin Duniya (UNCTAD) ya bayyana cewa, barkewar annobar ta janyo durkushewar tattalin arziki a duniya data kai dala tiriliyan daya a wannan shekarar.
Har ila yau, sashen na UNCTAD ya ce, annobar ta coronabirus ta janyo cikas ga hada- hadar kasuwanci a fadin duniya, inda hakan zai janyo aka samu raguwar fitar da amfanin gona da kudin su ya kai dala biliyan 50 a daukacin fadin duniya.
A watan da ya gabata, wasu daga cikin masu fitar da kayan zuwa kasasyen waje sun fuskanci samun raguwar fitar da kayan ganin cewar, kasashen sun rufe iyakikin su da kuma bayar da marnin soke dukkan hada-hadar kasuwanci saboda yaduwar annobar ta Covid-19.
Sakamakon wannan takaita tafiye-tafiyen saboda jin tsoron annobar ta COVID-19, lamarin ya shafi kasuwanci kamar na sayar da abinci a gidajen sayar da abinci, da a Otel- Otel, wuraren shakatawa, tashin jiragen sama, inda hakan kuma ya shafi fannonin samar da abinci da amfanin gona.
Bugu da kari, manyan kamfanonin dake yin safarar amfanin gona zuwa kasashen duniya kamar su Amurka, Jamani, Birtaniya, Singapore, Italy da kuma China, duk sun dauki matakai kannsanar da kariya ga abinci don kare yada annobar akan tattalin arzikin kasashen su.
Idan a ka yi la’akari da yadda annobar coronabirus ke yaduwa kamar gobarar daji, ta ragarza hada-hada a kasuwanin duniya, inda hakan ya sanya kwarru suka yi gargadi kan yadda annobar za ta iya shafar fitar da amfanin gona zuwa kasashen duniya.
daya daga cikin kwarren dake a jami’ar koyar da darasun aikin noma ta Ilorin (UNILORIN), Farfesa Abiodun Adeloye ya sanar da cewa, illar ta annobar zata iya janyo yin tafiyar Hawainiya ga bunkasar tattalin arzikin duniya da kuma shafar safar amfanin gona zuwa kasashen waje.
kwararren a jami’ar ta (UNILORIN), Farfesa Abiodun Adeloye yaci gaba da cewa, annobar ta coronabirus zata iya janyo hadari ga bukatar da ake da ta amfanin gona, mussmman ganin an ssnya takunkumin tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya inda tafi barkewar.
A cewar kwararren a jami’ar ta (UNILORIN), Farfesa Abiodun Adeloye ya sanya ran za’a sanu raguwar fitar da amfanin gona zuwa kasahen waje saboda barkewar annobar.
Shi ma Babban Sakatare a Cibiyar ayyukan fitar da kaya zuwa kasashen waje da kula dasu ta kasa (IEOMN) Mista Ofon Udofia, hada-hadar amfanin gonar ta shiga cikin matsala matuka.
Babban Sakatare a Cibiyar ayyukan fitar da kaya zuwa kasashen waje da kula dasu ta kasa (IEOMN) Mista Ofon Udofia ya kara da cewa, hatta tashoshin ruwa na kasa da kasa da juma ofishohin su ha abokan cinikayya suna yin dari-dari da kuma fuskantar matsaloli saboda takaita zirga-zirgar amfanin gona da kuma sauran kaya saboda annobar.
A karshe, Babban Sakatare a Cibiyar ayyukan fitar da kaya zuwa kasashen waje da kula dasu ta kasa (IEOMN) Mista Ofon Udofia ya ce, saboda barkewar annobar ta coronavirus.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: