Connect with us

MANYAN LABARAI

Yanzu-yanzu: Abokin Gwamnan Bauchi Ya Kamu Da Coronavirus

Published

on

A yanzu-yanzu, Kwamishinan lafiya na jihar Bauchi, Dakta Aliyu Maigoro, ya tabbatar da cewar sun sake samun mutum guda da yake dauke da cutar Coronavirus a jihar.

Wanda ya sake kamuwa da cutar Abokin gwamnan jihar Bauchi ne, duk da kawo yanzu hukumar lafiya ta jihar ba ta bayyana sunan wanda ya sake kamuwa da cutar ba.

Dakta Maigoro ta shaida hakan ne a taron manema labaru da suka kira da karfe 5:40pm a shalkwatan hukumar lafiya ta jihar, yana mai shaida cewar daga cikin mutum 37 da suka kai samfurin jininsu zuwa cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC, an samu tabbatar mutum biyu da suke dauke da cutar.

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan da NCDC ta tabbatar da cewar gwamnan jihar Bala Muhammad na dauke da cutar, inda aka sake samun karin mutum guda da yake dauke da cutar wanza kuma abokin gwamnan jihar ne bayan da suka yi mu’amala da shi.

Kwamishinan lafiyar ya kuma ce, yanzu haka za su dauki samfurin jinin dukkanin mutanen da wanda suka sake samu na dauke da cutar domin su ma a gwadasu ko suna da cutar ko a’a.

Dakta Maigoro ya ce, suna kuma jiran sauran sakamakon gwajin da suka dauka na mutune 9 kawo yanzu, sai dai ya ce suna ci gaba da daukan jinin mutane domin dakile yaduwar cutar.

Kwamishinan ya shaida cewar mai dauke da cutar na biyu mai shekaru 62 abokin gwamnan jihar Bauchi ne, “Abokin wanda ya kamu da cutar na farko ne, amma an killaceshi kawo yanzu,” A cewar shi.

Karin bayani kan labarin na tafe….
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: