Connect with us

RIGAR 'YANCI

Yau NURTW Kaduna Za Ta Fara Yekuwar Wayar Da Kai Kan COVID-19

Published

on

Domin kawo karshen wannan cuta ta Konora 19, da kuma ilmantar da direbobi da ma su shiga tashoshin mota a kananan hukumomin jihar Kaduna 23, kungiyar direbobin motocin haya reshen jihar Kaduna za ta fara gangami na musamman.

Shugaban kungiyar reshen jihar Kaduna Alhaji Akiyu Tanimu Zariya ya bayyana wa wakilinmu tsare-tsaren da suka sa wa gaba, domin kare direbobi da ma su shiga motocin haya da kuma wadanda ke shiga motocin haya, domin tafiye-tafiye a ciki da wajen jihar Kaduna.
Alhaji Aliyu Tanimu ya ce, kungiyar NURTW a jihar Kaduna ta gayyato kwararrun likitoci da za su yi jawabai da kuma fadakarwa ga direbobi da kuma duk wanda ke cikin tashoshin mota da suke jihar Kaduna.
Ya kara da cewar, wannan tsari da su ke aiwatar wa babban motsi ne su ka yi, domin ganin duk wani direba da fasunjoji da su ke shiga tashoshin mota, sun sami ilimin rigafin day a kamata su yi da kuma matakan taimakon farko da suka da ce su sani, da zarar wani a kusa da su, ya kamu da wannan cuta.
Baya ga jawaban da likitocin za su yi, a cewar Alhaji Aliyu Tanimu, kungiyar za ta kuma jagoranci taro na musamman da daukacin shugabannin kungiyar na kananan hukumomin jihar Kaduna 23, muhimmancin wannan taro, a cewarsa, shi ne da zarar an kammala taron shugabannin kungiyar na kananan hukumomi  su koma kananan hukumominsu, domin aiwatar da ilimin da su ka samu daga likitocin da suka yi jawabi kan wannan cuta ta COVID-19.
Alhaji Aliyu Tanimu Zariya kara da cewar, saboda wannan cuta da ta zama babbar matsala ga duniya baki daya, ya ce, sun dauki matakan rage yawan fasunjojin da ake dauka a motocin haya,a cewarsa, kamar motar da a ke daukar mutum goma a koma daukar mutum takwas, wadda ke daukar mutum shida ta dauki mutum hudu, wannan kamar yadda ya ce zai matukar tasiri na rage bunkasar wannan cuta, kamar yadda gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar Kaduna suka saw a gaba, na kare al’umma da kamuwa da wannan cuta.
A karshe, Alhaji Aliyu Tanimu ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Kaduna, da su sa kungiyar direbobi a cikin tsare-tsaren dakushen wannan cuta, musamman a duk wasu ayyuka da za a aiwatar da su ka shafi tashoshin mota da su ke kananan hukumomin jihar Kaduna 23.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: