Connect with us

LABARAI

Za A Kama Duk Wanda Ya Je Masallacin Juma’a Gobe -Hon. Yahaya Sirika

Published

on

Gwamnatin jihar Katsina ta ce doka zata yi aiki akan duk wanda ya yi gigin karya dokar hana zuwa masallacin juma’a gobe wanda aka sanyi a matsayin daya daga cikin matakan kariya daga kamuwa da cutar mahsako

Kwamishinan yada labaru da al’adu na jihar Katsina Hon. Abdulkarim Yahaya Sirika ya bayyana haka a wata zantawa da ya yi da manema labarai a Katsina.

Hon. Yahaya Sirika ya ce ba wai zuwa Massalacin juma’a kadai akan hana ba, an hana zuwa mujami’a a ranar lahadi kamar yadda Kiristoci suka saba zuwa, sannan an hana taron biki da taron siyasa ya ce duk wani taro da zai hada jama’a a waje guda an haramta shi yanzu.

Ya ce wannan doka anyi ta sakamakon bullar wannan cuta ta Corona Birus ko Cobid 19 amma ba wai gwamnati ta yi hakan ba domin kuntatawa jama’a ba, ta yi ne domin ta tsare rayuwa da kuma dukiyoyin jama’a

“Wannan doka zata cigaba da wanzuwa har zuwa lokacin da muka ga wannan al’amari ya kwaranye, kuma muna sane da cewa riga kafi yafi magani, sannan duk inda ku ga wannan cuta ta yawaita to lallai akwai rashin daukar matakai irin wannan da muke dauka” inji shi.

Sai dai ya ce akan maganar hana cin kasuwanni har yanzu ba su hangu wata matsala ba dangane da sha’anin kasuwanni saboda haka sai nan gaba ne za su duba yiwuwar hana cin kasuwanni, amma dai yaznu ga sanarwa da suka ba, abubuwa ne da yawa za su rika zuwa daya bayan daya.

Haka kuma kwamishinan yada labaran ya ce su biyar ne gwamnan Masari ya dorawa alhakin yin wannan aikin kuma an ba su sati daya ne su kammala wannan aiki da ke gaban su.

Hon. Yahaya Sirika ya ce abubuwan da aka umarce da su shi ne, su zagaya wuraran kasuwanci suna sanar da jama’a yadda ya kamata su gudanar da sha’anin kasuwancinsu domin kauracewa kamuwa da wanna cuta ta Corona Birus
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: