Connect with us

TATTAUNAWA

Za Mu Hada Hannu Da Gwamnatoci Don Fatattakar Ciwon Suga – Dr. Usman

Published

on

DR. NURADDEEN USMAN, shi ne Shugaba Cibiyar Bayar da maganin cutar Siga (diabetic), gogaggen matashin Likitan Gargajiya wanda masana suka aminta da sahihancinsa, wanda kuma Hukumar da ke lura da abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), ta amince da sahihancin magungunansa, sannan ta sahale masa bude wannan Cibiya, domin duba masu fama da wannan lalaru ta ciwon Siga. Dakta Nuraddeen, a tattaunawarsa da Wakilin LEADERSHIP A YAU a Kano, ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, ya bayyana wannan matsalar cuta ta siga da cewa, cuta ce mai tsananin keta wadda ba kasafai a ke gane ta a matakin farko ba, idan ba zuwa aka yi wurin kwararru ba. Likitan ya bayyana matakan da a ke bi, domin magance matsalar tun tana karama kafin ta yi illa ga rayuwar al’umma. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:

Za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatu?
Alhamdulillahi, sunana Dakta Nuraddeen Usman, Shugaban Cibiyar da ke bayar da magungunan Cutar Siga (Diabetic Herbal Medicine Center), tare da gudanar da bincike mai zurfi, wadda ta shahara wajen taimakawa al’umma domin magance wannan lalura.

Kamar yadda ka bayyana cewa, wannan Cibiya ce da ke bayar da magungunan ciwon Siga, kenan tana da alaka da maganin gargajiya?
Babu shakka, wannan magani ne na gargajiy amma na zamani, kamar yadda a ka sani magungunan gargajiya sun kasu kashi biyu, akwai magungunan gargajiya wanda masana a duniya wadanda su ka yi karatu mai zurfi har suka kai matakin samun Digiri da Digirgir. Wadanda kuma su ka gudanar da bincike mai zurfi kan tsirrai, ganye, bishiyu masu alaka da kuma maganin gargajiya. Wadanann kwararru suna da yawa a kasashen duniya da ya hada da Amurka, kasashen Tarayyar Turai, China, Maleshiya da kuma Korea, masana ne wadanda tarihinsu ya tabbatar da kwarewarsu.
Wasu daga cikinsu Likitoci ne irin na zamani, amma saboda yadda cutar ke bujirewa magunguna, yasa masanan su ka tsunduma cikin harkar magungunan gargajiya, domin samawa al’umma mafita, inda suka gudanar da bincike kan ganyayyaki, wadanda asalinsu abinci ne. irin su yadiya, zogale, dinkin tafasa, kabeji, gurji, mangwaro, ganyen ayaba da kuma na lemo, akan wadannan abubuwa suka gudanar da gagarumin bincike har kuma aka hadu akan samar da irin wannan magunguna masu tasirin gaske ga lafiyar al’umma.

Shin Likita, mece ce ne cutar Suga (Diabetic)?
Ciwon Siga shi a ke kira da ‘Diabetic’ a turance, da farko a na iya samun wannan ciwo ta hanyar gado ko kuma wanda Allah Ya jararba da shi, ciwo ne da ake kamuwa da shi ta hanyar cin kayan zaki ko sha ko kuma yawan cin abinci mai alaka da zaki. Misali, masara tana da sinadarin sikari mai karfi ajikinta, don haka yawan cin tuwon masara na iya haifar da matsalar ciwon Sugar. Sannan farar dawa akwai sinadarin Siga a cikinta kwarai da gaske, shinkafa kuma akwai sinadarin sitati a cikinta, wanda ke zuzuta matsalar ciwon na Siga.
Haka nan, taliya, macaroni da Indomie, dukkaninsu suna dauke da irin wannan sinadari. Sannan kuma, ga irin kayan zaki da ake sha a koko, shayi, Fura da sauran makamantansu. Kazalika, shan nau’o’in wadanann kayan zaki da ake sha a kullu yaumun suke taruwa, kana kara girma suna karuwa, a karshe sai su tararwa mutum
su haifar masa da matsala. Ita wannan cuta ba a iya gane ta kai tsaya, domin cuta ce mai ketar gaske.

Kamar yadda Likita ka yi bayanin wannan cuta na da alaka kai tsaye da cimarmu, idan haka ne ta yaya mutum zai iya gane cewa ya kamu da wannan cuta ta Suga?
Alama ta farko ita ce, yawan fita fitsari da daddare kamar sau biyar zuwa goma, sai kuma ramar jiki, kasalar jiki, ciwon gabobi, raguwar gani, kasancewa kullum cikin raunin jiki wanda baya gushewa, wadannan suna cikin alamomin da ke tabbatar da cewa kana da wannan ciwo na Siga.

Wane mataki mutum ya kamata ya fara dauka idan ya fahimci ya kamu da
wannan ciwo na Siga?
Mataki na farko shi ne, zuwa Asibiti domin yin gwajin jinni da fitsari, ta nan ne za a iya fahimtar karfin cutar, daga nan kuma za a dora shi akan magani. Ta fuskarmu kuma, wannan Cibiyar na gudanar da bincike tare da bayar da magungunan wannan cuta, wadda yanzu haka muke kan titin Zariya kusa da katafare kantin sayar da kayayyakin nan Jifatu, muna kuma bayar da magungunan wannan cuta wadda Hukumar da ke lura da abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), ta amince da nagartar magungunanmu bayan gudanar da cikakken bincike kansu da
wannan Cibiya ta samar, domin magance wannan cuta ta Siga, suka kuma amince
tare da ba mu shaidar amincewa, sannan suka yarda mu cigaba da bayar da magani a fadin wannan da ma duniya baki-daya.

Mene ne banbancin maganin Siga na gargajiya da kuma na bangaren Likitancin zamani?
Mu namu an aminta da shi tare da gamsuwa cewa, ana warkewa baki-daya daga wannan cuta, yayin da kuma shi na Bature ake cigaba da sha har tsawon karshen rayuwa. Wannan shi ne banbancin da ke tsakaanin nasu da kuma namu.

Likita, ta yaya a ke fara yin mu’amala tsakanin mara lafiya da wannan Cibiya?
Kamata ya yi mutum ya zo da kansa wannan Ofis namu ya bude fayal, sannan ya yi rijista da mu, tare da daukar dukkanin bayananka. Daga nan, sai mu gwada jininka, fitsari, yanayin jikinka, tsawonka da dai sauransu. Idan aka tababtar da wadannan abubuwa, sannan sai a dora ka akan magani.

Ganin yadda wurin naku yake, anya kuwa mai karamin karfi ka iya samun damar ziyartar ku, domin neman magani?
kwarai kuwa, ina tabbatar maka da cewa kowa na iya zuwa wurinmu, domin mun tanadi dukkannin wani rangwame, bari ma ka ji wani taimako da wannan Cibiya ke bayarwa, ko a ranar Asabar da ta gabata, don taimakawa kokarin Gwamnati na magance matsalolin lalurar wannan cuta ta Siga, sai da muka duba yin gwaje-gwaje tare da bayar da magani kyauta ga mutane 100 a wannan Cibiya, kuma yanzu haka mun tsara ranar biyar ga watan Ramadan, domin taimakawa al’umma.
A wannan lokaci idan Allah Ya kai mu, za mu yi wa mutane 100 gwaje-gwaje tare da ba su magunguna kyauta. Sannan, idan Allah Ya kai mu sha biyar ga watan Ramadan, nan ma za mu yi irin wannan aiki kyauta tare da bayar da magunguna kyauta, sai kuma a karshen watan za mu maimaita kamar haka. Kazalika, mun tsara taimakawa al’umma mutum 300 a watan nan na Azumi mai zuwa kadai. Saboda haka, wannan Cibiya akwai kyawawan tanade-tanade da ta yi wa mai karamin karfi.

Ganin irin wannan lokaci ne na siyasa, shin ko kuna da wani tsari da masu rike da madafun iko, domin hada karfi da wannan Cibiya tare da samar da wani tsari wanda zai rika daukar nauyin al’ummar da yake wakilta, musamman masu fama da wannan lalura?
Wannan ne dalilin yin wancan aiki na ranar Asabar da ta gabata, domin nunawa Gwamnati da masu rike madafun ikon cewa, a shirye muke wajen hada hannu da su domin tallafawa al’ummarmu wajen yaki da wannan cuta da ke illata al’umma. Wannan tasa muka fara da kanmu, domin zama wata fitila da ka iya haskawa duk wanda ke bukatar tallafawa harkokin lafiyar al’umma.

Wacce shawara a matsayinka na kwararre akan wannan harka za ka baiwa al’umma domin rigakafin wannan cuta?
Da farko dai, yana da kyau jama’a su lura kwarai da gaske wajen cimarsu, sannan a mayar da hankali wajen yin amfani da ganyayyaki, su zama su ne suka fi yawa a cikin abincinmu, kamar ganyen alayyahu, Ogbu, lamsir, salat, zogale, karas, gurji, ayaba da lemo, sannan a yawaita cin wake a cikin abincinmu na yau da kullum. Sai kuma dagewa wajen motsa jiki.
A wannan gaba, ina rokon gwamnati ta yi la’akari da halin da jama’a ke ciki, musamman kan wannan cuta da aka yi ittifaki cewa cikin mutune goma, mutum shida na dauke da ita, kuma da yawa ba su san suna da ita ba, har sai ta kazanta sannan a runtumo zuwa ga Likita neman magani, amma idan al’umma suka rungumi wadancan shawarwari da muka bayar, ta hanyar ziyartar wannan Cibiya za a samu kwararan shawarwari, wanda idan aka yi aiki da su za a yi bankwana da wannan cuta baki-daya.
Har ila yau, ina kara jinjinawa gwamnatoci bisa kokarin da suke yi na samar da hanyoyin duba lafiyar al’umma, wanda a wannan lokaci duniya ta fahimci cewa babbar mafita ga matsalolin cututtukan da ke bujirewa magunguna su ne yin amfani da magungunan gargajiya a irin wannan lokaci da masana ke gudanar da cikakken bincike tare da inganta tsarin bayar da maganin, wanda ya yi daidai da matsayin kowane iri da aka aminta da shi wajen bayar da magani. Don haka, wannan Cibiya ta samu cikakkiyar shaidar cigaba da bayar da magunguna a kowane mataki tun daga kan jiha, kasa da ma duniya baki-daya.

Mun gode.
Ni ma na gode.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: