Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Zamba: Kotu Ta daure Shugaban Hukumar Ibadar Kiristoci Shekara Biyar

Published

on

Wata babbar kotun jihar Adamawa, ta daure tsohon shugaban hukumar jindadin aikin ibadar kiristoci ta jihar (ASCPWB) Biship Jingi Mayo, shekaru biyar, bisa samunsa da laifin zamba cikin aminci lokacin da ya kasance a matsayin shugaban hukumar a 2016.

Malam Bello Bakori, shugaban hukumar yaki da munanan ayyuka da zargin aikata miyagun aiki ta kasa (ICPC), ya bayyana haka ranar talata, cikin wata takardar sanarwar manema labarai a Yola.
Sanarwar ta cigaba da cewa Bishop Jingi, ya taba zama babban sakataren gudanarwar hukumar jindadin aikin ibadar kiristoci ta jihar a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017, kotu ta mishi daurin gyara halinka ba bisa zabi ba ranar 23 ga Maris 2020.
Ya ce kotu ta caji wanda a ke zargi ne da caji mai lamba 3 wanda a ka gabatar ranar 30 ga Junairun 2019, wanda ya saba da tanadin doka na 16, 19 da 25 (1) (a)  na humumar ICPC.
Hukumar ta ce cajin da kuma hukuncin suna karkashin doka mai lamba 16, 19 da 25(1)(b) na dokar yaki da munanan ayyuka, da dabi’u marassa kyau ta shekarar 2000.
Ta ce, “wanda a ke zargi an kai shi kotu ranar 3 ga Janairu, 2019, bisa karkatar da kin dawo da kudi naira miliyan sittin da tara, da dubu dari da casa’in da takwas da naira dari shida (N69,198,600.00).
“Kudaden bayan gudanar da bincike mun gano kudaden gudabar da kwamitoci ne a aikin ibada kasar Isra’ila a shekarar 2016, amma bisa zamba wanda aka dauren ya maishe da kudaden biyan bukatun kanshi.
“Babbar kotun jiha karkashin Mai Shari’a Nathan Musa ta daure shi tsawon shekaru biyar a gidan yari bisa karkatar da kudaden gwamnati da bada bayanan karya ga hukumar” in ji sanarwar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: