- Jam’iyyar Za Ta Fara Sabbin Rijistar Mambobi 12 Ga Disamba
Daga Khalid Idris Doya
A wani mataki mai kama da cigaba da mike kafa a mulkin kasar, Jam’iyyar APC da ke mulkin Nijeriya ta shaida cewa, za ta fara sabuwar rijistar mambobi gami da sabunta shaidar zama dan jam’iyya daga ranar Asabar, 12 ga Disamba, 2020, zuwa Asabar 9 ga Janairu, 2021.
Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar wanda kuma shi ne Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, shi ne ya shaida hakan a jiya ta cikin sanarwar da ya raba wa ’yan jarida a Abuja, ya na mai cewa, hakan ya biyo bayan shawara da tuntubar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ciki har da Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari kan gudanar da aikin yin rijistar.
A cewarsa: “Mun tuntubi masu ruwa da tsaki ciki har da mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari, fara aikin rijistan sabbin mambobin APC da kuma sabunta katin shaidar zama dan jam’iyya zai gudana a tsakanin ranar Asabar 12 ga watan Disamban 2020 zuwa ranar Asabar 9 ga watan Janairun 2021.
“Kan hakan, kowani mamban jam’iyyarmu ana gayyatarsa da ya sabunta katin zamansa dan jam’iyya a gundumarsa. Har-ila-yau wadanda suke sha’awar kasancewa a cikin jam’iyyarmu mu na gayyatarsu da su yi amfani da wannan damar wajen yin rijista domin shiga ciki jam’iyyarmu.
“Rijistan sabbin mambobin jam’iyya da sabunta shaidar zama dan jam’iyya zai gudana ne a lokaci guda a kowace gunduma da ke fadin kasar nan.”
Ya kuma ce za su tabbatar da kayayyakin gudanar da aikin rijistan sun isa kowace gunduma a kam lokaci, “Aikin rabar da kayan gudanar da ayyukan rijista da sabunta shaidar zama dan jam’iyyar za a raba su ga dukkanin jihohin kasar nan, kananan hukumomi, gundumomi da gundumomi kafin ranar 12 ga Disamban 2020, ranar fara gudanar da rijistan.”
Sai sanarwar ta roki jagororin jam’iyyar a jihohi, kananan hukumomi da gundumomi da su tabbatar da yin duk mai yiyuwa domin tabbatar da aikin sabuntawa da yin rijistan jam’iyyar ya gudana cikin kwanciyar hankali da dadin rai.
Shugaban kwamitin rikon ya sha alwashin cewar za su cigaba da sanar da jama’a halin da ake ciki kan shirye-shiryen yin rijistan domin jama’a su zama suna da cikakken masaniya a kai kamar yadda ya ke bisa doka.