2023: Atiku Da Tambuwal Sun Bukaci 'Yan Nijeriya Ka Da Su Sake Zabar APC
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: Atiku Da Tambuwal Sun Bukaci ‘Yan Nijeriya Ka Da Su Sake Zabar APC

byAbubakar Abba
3 years ago
Atiku

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da ka da su sake zabar jam’iyyar APC a zaben 2023.

Atiku, ya yi wannan kiran ne cikin sanarwar da kakakin PDP a Jihar Sakkwato, Hassan Sanyinnawal, ya fitar, inda ya ce, Atiku ya yi gargadin ne a jawabin da ya yi a taron masu ruwa da tsaki da ya  gudana a Jihar Kano.

  • Ba Zan Bari Kowa Ya Kawo Cikas A Zaben 2023 Ba – Buhari
  • Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Gana Da Jonathan, Ya Nemi Ya Mara Masa Baya

Atiku ya ce idan ‘yan Nijeriya suka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023, zai magance kalubalen rashin tsaro, hauhawar farashin kayan masarufi, inganta fannin ilimi da sauransu.

A cewarsa, APC ta rasa inda za ta fuskanta da yin tunani kan yadda za ta lalubo da mafita kan matsalolin da Nijeriya ke ci gaba da fsukanta, inda ya yi nuni da cewa, hakan ya nuna a zahiri, APC ta gaza.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban kungiyar gwamnonin PDP, gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayar da tabbacin cewa, nasara na tare da PDP a daukacin jihohi bakwai da ke a yankin na Arewa Maso Yamma.

Tambuwal ya ce APC ba ta da wata hujjar sake yi wa ‘yan Nijeriya kamfen ganin cewa ta gaza, inda ya ce duk mai tunani ba zai sake zabar APC ba.

Wasu daga cikin mahalarta taron, su ma sun gargadi ‘yan Nijeriya kan sake zabar APC a zaben 2023, musamman inda suka danganta irin halin kuncin rayuwa da APC ta jefa ‘yan Nijeriya a ciki.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas
Labarai

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas

October 2, 2025
Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara
Siyasa

Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara

September 28, 2025
Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas
Siyasa

Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas

September 27, 2025
Next Post
Direban Adaidaita Sahu Ya Mutu A Rafi A Kano

Direban Adaidaita Sahu Ya Mutu A Rafi A Kano

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version