2023: Ba Wanda Muka Tsayar Takarar Gwamnan Kano Zuwa Yanzu – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce har yanzu jam’iyyar PDP da Kwankwasiyya ba ta yanke shawarar wanda zai tsaya mata takarar gwamna a shekarar 2023 ba.

Sanata Kwankwaso ya yi bayanin hakan ne yayin tattaunawa da jagororin Kwankwasiyya biyo bayan rashin jituwar da ta faru a makon da ya gabata tsakanin mabiya Kwankwasiyyar.

An rawaito cewa, rabon kayan tallafin azumi da Dakta Yunusu Adamu Dangwani ya yi da azumi ya haifar da rashin jituwa a Kwankwasiyya, inda wadanda ke goyan bayan takarar da Abba Gida-gida ke zargin Dan Gwani da yakar Kwankwaso. A wani didiyo da ya yadu an ga sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP, Sanusi Surajo Kwankwaso na zargin Dan Gwani da haifar da rabuwar kai a kungiyar saboda muradinsa na neman takarar gwamnan Jihar Kano. Sai dai a martanin da ya mayar, Dan Gwani ya musanta batun cewa yana neman takarar gwamnan inda ya ce lokaci bai yi ba a halin yanzu.

Sai dai a zaman tattaunawar da ya gudana ranar Litinin a Miller Road da ke cikin garin Kano, Kwankwaso ya bayyanawa masu ruwa da tsaki a Kwankwasiyya da jam’iyya ba ta da dan takara a shekerar 2023 a yanzu, inda ya yi bayanin cewa idan lokaci yayi jam’iyyar za ta bi hanyar dimukuradiyya wajen fitar da dan takara. A yayin zaman tattaunawar, Kwankwaso ya jaddada cewa babu wani dan takara a yanzu don haka kowa ya tsaya a matsaya guda.

Exit mobile version