Tsohon gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindow, ya bukaci mambobin jam’iyyar APC, da su hadakai domin fuskantar manyan zabukan dake tafe na shekarar 2023.
Bindow ya bayyana haka ne, lokacin da ya ziyarci sakatariyar jam’iyyar APC dake Yola, ranar litinin, ya ce lamarin mulki lamari ne daga Allah, saboda haka akwai bukatar hadakai da aiki tare domin don samun nasarar jam’iyyarsu.
Haka kuma gwamnan ya bayyana dalilin da yasa ya dauki lokaci mai tsawo ba tare da kasancewarshi a jihar ba, da cewa hakan ya faru ne domin zaman lafiya, da kuma sha’anin tsaro, da ci gaban jihar.
Tsohon gwamna Bindow, ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyyar da su kokarin gudanar da aikin sabonta katin yayan jam’iyyar da yayansu da iyalansu baki daya, ya ce su ko da wasa kada su yanki katin sau biyu.
Haka kuma shugaban ya yabawa tsohon gwamnan da sauran ma su rike da mukaman siyasar bisa samar da aikinyi ga matasa da shirye-shiryen da su ke yi wanda kai tsaye jama’ar jihar ke amfana dashi.
Bilal, ya tabbatar da cewa akowani lokaci jam’iyyar APC zata tabbatar ta yiwa yayanta adalci da gaskiya, ya ce “abinda mutane su ke so zabin da jama’a su ka yi shi jam’iyya zata basu.
“Manyan mutane da dama su na canja sheka su na dawowa jam’iyyarmu, wasu manya da dama su na shirye da su shigo, muna kan tuntuban wasu mutanen,” inji Bilal.