Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home LABARAI

2023: Gwamna Bala Ne Ya Fi Cancantar Shugabancin Nijeriya – Wata Kungiya

by Sulaiman Ibrahim
March 15, 2021
in LABARAI
2 min read
2023: Gwamna Bala Ne Ya Fi Cancantar Shugabancin Nijeriya – Wata Kungiya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Wata kungiyar siyasa ta bukaci gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir da ya ayyana gami da amsar kiran fitowa neman takarar Shugaban kasar Nijeriya a lokacin Babban zaben 2023.
Wannan kira ya fito daga bakin wata kungiya siyasa ce mai da’awar ‘yar bangan Bala Abdukadir Mohammed a karshen wani taron ta da ta gudanar a garin Bauchi, tana mai cewar, Gwamna Bala shine mafi cancantar shugaba da ya dace da kasar nan.
Shugaban kungiyarta, Kwamred Mohammed Abubakar Jibo wanda ya yi jawabi a wajen taron, ya lura da cewar, Nijeriya a halin yanzu tana fuskantar kalubale masu yawa wadanda Gwamna Bala Muhammad zai iya shawo kansu matukar an zabe shi a matsayin shugaban kasa.
kungiya don haka ta yi kira ga Gwamna Bala Mohammed da ya amsa kiranta na kasancewar dan takaran Shugaban kasa a zaben gama-gari mai zuwa na shekara ta 2023, tana mai cewar “Tabbas jihar Bauchi tana bukatar Bala Mohammed domin yin zango na biyu na Shugabanci, amma kasar tafi bukatar sa fiya da jihar Bauchi, don haka ya zama wajibi mu roke shi domin amincewar sa bisa wannan mukami da muke sonsa da shi.”
Kamar yadda Jibo ya ce, daga cikin wadanda a shirrance suke bukatar takarar kujeran shugabancin kasar nan, Bala Muhammad shine mafi cancanta ya kasance Shugaban kasa na gaba wa kasar.
Ya kuma ce, daukan wannan matakin kiran gwamnan ya fito neman shugabancin kasar, ya biyo bayan tuntubar masu ruwa da tsaki a kuma duba kyawawan ayyukan raya al’umma da Gwamna Bala Muhammad ya gudanar a yayin da yake ministar Abuja da yanzu da ake gwamnan jihar Bauchi.
Ya ce, kungiyar an shirya ta ne domin tabbatar da kyakkyawar shugabci da wakilci na kwarai a tsakanin jama’a, a bisa hka ne suke da yakinin idan gwamnan jihar Bauchi ya zama shgaban Nijeriya su na da yakinin za  samu cigaba da sai ma daurewa a kasar nan.
kungiyar ta nuna fushinta kan yadda lamura suke tafiya ba daidai ba a kasar nan, don haka suka roki Sanata Bala da ya fito cikin jerin masu neman shugabancin Nijeriya a 2023.

SendShareTweetShare
Previous Post

Ambaliya: Kungiyar KDF Ta Raba Hatsin Naira Miliyan Biyu A Kebbi

Next Post

Buhari Ga ‘Yan Bindiga: Ba Za Mu Bari Ku Tarwatsa Mana Tsarin Karatu Ba

RelatedPosts

Isra’ila Ta Kai Hare-hare A Zirin Gaza

Isra’ila Ta Kai Hare-hare A Zirin Gaza

by Sulaiman Ibrahim
9 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim Isra'ila ta ce ta kai harin bama-bamai...

Yadda Sojoji Suka Kashe Kwamandan ISWAP A Damasak

Yadda Sojoji Suka Kashe Kwamandan ISWAP A Damasak

by Sulaiman Ibrahim
9 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim Wani babban kwamandan ISWAP, Bukar Gana (wanda...

NDLEA

NDLEA Ta Sanar Da Fara Kai Farmaki Dakunan Hada Muggan Kwayoyi

by Muhammad
13 hours ago
0

Daga Bello Hamza, Shugaban hukuamar NDLEA Birgediya Janar Buba Marwa...

Next Post
Minista

Buhari Ga ‘Yan Bindiga: Ba Za Mu Bari Ku Tarwatsa Mana Tsarin Karatu Ba

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version