2023: Gwamnonin Kudu Sun fi Na Arewa Nuna Kishi (2)

Tare Da El-Zaharadeen Umar,

Kamar yadda na yi alkawari cewa a wannan makon zan cigaba da wannan rubutu kuma na yi bayanin cewa matsaya ko matakin da gwamnonin kudu suka dauka abu ne da yake nuna yadda suka san kan su sannan suka damu da bukatarsu da ta mutanen su.

Daga cikin abubuwan da suka bayyana a matsayin abinda za su yi aikin da shi wajan cimma wannan matsaya babu abu daya da zai amfanin yankin arewa ko su kan su ‘yan arewan in banda maganar kasancewar Najeriya kasa daya al’umma daya.

Kuma yarda da wannan matakin ko matsaya zai taimaka wajan samun nasara manufofinsa na siyasa na fili da kuma na boye, tunda ba a san iya abinda suka da shi a cikin wannan motsi ko yunkuri na su ba.

Babu shakka arewa da shuwagabaninta sun yi barci mai nauyin gaske, an bar su a baya, a kyalesu da taruwa waje guda domin amsar wanda ya canza jam’iyya daga APC zuwa PDP ko daga PDP zuwa APC ko kuma idan za a baiwa wani Sarkin sandar girma ko kuma daurin auran ‘ya ‘yan manya.

Kamar yadda na ce zan kawo duk abubuwa da suka bayyana a matsayin matakin da za su dauka wajan ganin sun kai ga cimma nasara, sannan ayi masu kallon kurilla domin ganin inda wannan siyasa ta dosa ko ba komi an yi walkiya halin kowa ya bayyana.

Tun a labarin da mafiyawan jaridu suka buga wanda ya ja hankali kuma yake cigaba da tada muhawara shi ne yadda suka bayyanawa duniya cewa tilas Ɗan kudu ne zai yi shugabancin Najeriya a zaɓen 2023

Sannan ba su duba cewa kila wannan batu ya jawo tarnaki a siyasar su ba, kuma idan aka duba sune suka ci gajiyar wannan gwamnatin fiye da kowa a Najeriya, amma suna ganin hakan bai ishe su ba, sai sun samu shugaban kasa ya fito daga yankin kudu sannan za su gamsu da abinda suke bukata a siyasa, ko me yasa haka oho!

Bayan kammala taron da gwamnonin yankin kudu gaba ɗayan su suka halarta a jihar Legas ranar litinin 5 ga yuli, 2021, sun bijiro da wasu buƙatu, sharuɗɗa da kuma matsayar su a kan batutuwan da su ka shafi siyasar su kaiwa, ba tare da duba yanayin da kuma halin da wannan kasa ta samu kanta ba.

Gwamnonin sun yarada cewa Najeriya ta ci gaba da kasancewa dunƙulalliyar ƙasa ɗaya, amma a bisa haɗin kai, kaunar juna, gaskiya da gaskiya, adalci da kuma raba-daidai gwargwado na arzikin ƙasa da muƙamai, saboda haka ko ba komi za su amfana idan haka ta samu kasancewa.

Haka kuma sun kafe kai da fata cewa lallai ilahi a riƙa gudanar da ingantacciyar siyasa nagartacciya, ba tare da maida wani ɓangare saniyar-ware ko gugar-yasa ba. A kan haka, sun cimma matsayar lallai ɗan kudu ne zai yi shugabancin Najeriya a zaɓen 2023.

Idan aka duba so sai, kamar wannan kalamai na su yana da alaka da kurman baki, domin ba su bayyana a wace jam’iyya ne dan kudun zai shugabancin Najeriyar ba, suna maganar dole dan kudu ya zama shugaban kasa, bayan kuma akwai jam’iyyun siyasa da za su iya fitar da dan takara kuma ya samu nasara daga yankin arewa, saboda haka babu ruwansu da wannan su dai a zabi koma wanene daga yankin kudu.

Wannan shi ne ake cewa yankan shakku da wadannan gwamnoni suka yi wa kan su, sannan suka bijiruwa da yankin arewa ko dai su amince da wannan matsaya ta su kuma wani abu ya biyo bayan hakan, domin idan ba haka ba, ta ya ya zaku zauna ku yanke hukuncin abinda ya shafi kasa baki daya ba tare da tuntubar sauran bangarori ba.

Ko shakka babu wannan ya kara nuna irin rauni da koma bayan wannan yanki na arewa domin har zuwa yanzu da nake wannan rubutu babu wani kakkausar martani daga wadanda ake kira ‘yan kishin arewa ko kuma su shuwagabanin arewa wato gwamnoni.

Ya kamata ya zuwa yanzu a ce sun ji wani sabon labari mai dadi daga bakin gwamnonin arewa akan wasu kudiruri da za su taimakawa wannan yanki da yake fuskantar kalubake iri-iri amma shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu.

Baya ga hakan sun kara da cewa sun amince a riƙa yin tsarin karɓa-karɓa tsakanin kudu da arewa ba tare da tabbatar da hakan ba ta hanyar bin wani tsari na doka ta kasa ba wanda kowane bangare zai amince da shi ba, a’a suna ganin hakan zai amfane su tare da jama’ar su na arewa kuwa ko oho!.

Dangane da matsalar tsaro kuwa cewa suka yi “mun jinjina wa jami’an tsaro, sannan sun yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda su ka rasa rayukan su. Kuma sun yi jaje ga waɗanda aka raunata, amma ba mu ji gudunmawar da suka ce sun bada ba.

“Mun jaddada buƙatar a bar kowace jiha ta kafa ƴan sandan ta” inji su ke nan, ko shakka babu wannan ba wanda zai amfana sai su, domin sun nuna alamar suna san yin haka kuma sun shirya ta hanyar kirkirar jami’an tsaron Amotakun da sauransu abinda har gobe ya gagari arewa da ‘yan arewa.

Duk da cewa gwamnatin shugaba Buhari na kauda kai da jin kunyar kama wadanda suke neman zame mata barazana a harkokin tsaro kuma ana barin su suna shan iska, gwamnonin sun kafe cewa tilas idan jami’an tsaro za su yi wani aikin kame ko farmaki a wata jiha, to a fara sanar da gwamnan jihar tukunna.

Gwamnonin Kudu sun yi tir da abin da su ka kira nuna fifiko da nuna bambanci wajen yadda gwamnatin tarayya ke daƙile wani ɓarin masu laifi ta kauda kai ga wani ɓangare na masu laifin. Sun ce duk wanda jami’an tsaro za su kama, to a riƙa bin matakin da doka ta gindaya, ba tare da danne haƙƙin ɗan Adam ba.

Wannan fa sune suka amfana da haka, domin a yankin arewa, inda shugaban kasar ya fito ba su da wannan gatan na cewa a bi tsari ko doka wajan kama mai laifi, sune ke da tarihin boye mai laifin ko hana aka mashi, amma wannan yana cikin agandojinsu. zan cigaba Insha’Allahu sati mai zuwa.

Exit mobile version