Daga Sulaiman Ibrahim
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta karyata rahotannin kafafen yada labarai kan shirin dawo da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin wanda ke dauke da tutar shugabancin jam’iyyar a shekarar 2023.
Sakataren yada labaran Jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiya, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da amsa tambayoyi kan shirin jam’iyyar na ba Atiku tikitin, a yayin tattaunawarsa da manema labarai a Abuja, ranar Laraba.
Kola ya ce a matsayinsu na jam’iyya, PDP a shirye take koyaushe don kare dimokiradiyya, kuma ba za ta yadda ta daura wa mutane dan takara ba.
“Ba mu fara sayar da fom ba, har sai lokacin yayi tukunna, ba mu san wadanda ke neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar ba a shekarar 2023. Bugu da kari, ba mu fara sayar da fom ba,” in ji shi.