2023: INEC Ta Samar Da Ingatattun Tsarukan Gudanar Da Tsaftataccen Zabe
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: INEC Ta Samar Da Ingatattun Tsarukan Gudanar Da Tsaftataccen Zabe

bySulaiman
3 years ago
INEC

Yanzu da zaɓen 2023 ke ƙara kusantowa, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa bijiro da wasu ƙwararan matakai huɗu da ta yi sun tabbatar da cewa babu wata hanya da za a iya bi a yi maguɗi anl zaɓen.

Mataki na farko shi ne dabarar tantance wanda ya yi rajistar mallakar katin zaɓe sau biyu ko fiye da haka, wato ‘Biomodal Voter Accreditation System’ (BVAS).

  • Mutum Miliyan 93.5 Ne Za Su Kada Kuri’a A Zaben 2023 – INEC

Na biyu shi ne amfani da na’urar tantance adadin masu zaɓe a rumfunan zaɓe, wato ‘INEC Voter Enrollment Device’ (IVED). Shi wannan tsari ya na maganin masu satar ƙuri’a ko ɓarayin akwatin zaɓe.

Na uku shi ne manhajar tattara sakamakon zaɓen da kowa zai iya gani ido-da-ido, wato ‘INEC Result Viewing Portal’ (IRVP).

Da ya ke magana a wurin taron zaburar da matasa muhimmancin zaɓe, wanda ƙungiyar Yiaga Africa ta shirya a Inugu, Mataimakin Sakataren INEC, Injiniya Chidi Nwafor, ya ce Dokar Zaɓe ta 2022 ita ce matakin hana maguɗin zaɓe na huɗu.

Saura kwana 116 a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar wakilai da na majalisar dattawa.

Idan ba a manta ba, a farkon Oktoba shi ma Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya tabbatar da cewa maguɗi ba zai yiwu a zaɓen 2023 ba.

A labarin, ya ce INEC ta fito da hanyoyin kashe maguɗin zaɓe.

Yayin da hukumar ke ci gaba da tsare-tsaren gudanar da zaɓubbukan 2023, shugaban ya bugi ƙirji da cewa INEC ta samu nasarar toshe duk wata ƙofar da za a iya bi a yi maguɗi.

Da ya ke jawabi a wani taron da aka shirya a Cocin St. James na Ɗariƙar Angalika da ke Asokoro, Abuja, a kwanan baya, Yakubu ya ce INEC ta samu wannan gagarumar nasara ne ta hanyar ƙirƙiro tsarin tantance mai rajistar zaɓe na ƙeƙe-da-ƙeƙe, wato BVAS.

Yakubu, wanda Mataimakin Kakakin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ba hukumar, Chukwuemeka Ugboaja, ya wakilta, ya tsarin tantance mai karin rajistar hikima ce da basirar injiniyoin INEC ta kai su ga kirƙiro shi.

Ya ce BVAS zai ƙara wa INEC ƙarfin gwiwar tabbatar da cewa ta shirya zaɓe sahihi, wanda babu yadda za a iya yin maguɗi a lokacin zaɓe.

Ya ce: “Abu na biyu da zai ƙara wa zaɓen 2023 inganci shi ne sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022. Sashe na 9 (6) ya bai wa INEC ikon daina yi wa mutane rajista kwanaki 90 kafin zaɓe. Daga nan ne kuma sai hukumar ta tankaɗe tare da tace rajistar ɗungurugum.

“Kuma mutane su fahimci cewa INEC ba ta iya soke rajistar kowa. Amma ta na da ikon soke rajistar wanda ya yi rajista sau biyu.

“Hanya ta uku da za a kawo ƙarshen maguɗin zaɓe ita ce aikawa da sakamakon zaɓe kai-tsaye ta na’urorin kafafen sadarwa na zamani daga rumfar zaɓe.

“Sannan kuma Sashe na 51 na Dokar Zaɓe ta 2021 ya nuna ƙin amincewa da sakamakon zaɓen inda adadin ƙuri’un da aka jefa a akwati su ka haura adadin yawan waɗanda aka tantance ta tsarin BVAS.

“Sannan kuma a zaɓen 2023, Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2023 ta haramta wa INEC karɓar sakamakon da aka tilasta wa jami’in zaɓe bayyana sakamkon zaɓe.”

Ya buga misali da zaɓen sanata na Jihar Imo a 2019, wanda duk da cewa tilasta jami’in INEC aka yi ya karanta sakamakon zaɓen, amma kotu ta amince da sakamakon. Ya ce a yanzu ƙarƙashin sabuwar dokar zaɓe, hakan ba zai yiwu ba.

Daga ƙarshe ya yi kira ga manya da masu ilimi mazauna birane cewa su daure su riƙa fita su na jefa ƙuri’a a ranar zaɓe.

Ya nuna damuwa kan cewa mazauna birane, musamman masu hali da manyan ‘yan boko, ba su zuwa su na jefa ƙuri’a, duk kuwa da cewa sun san muhimmancin yin zaɓen.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
PDP Ta Maka APC A Kotu, Ta Nemi A Kori Shugaban APC Na Kasa Daga Mukaminsa

PDP Ta Maka APC A Kotu, Ta Nemi A Kori Shugaban APC Na Kasa Daga Mukaminsa

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version