Daga Khalid Idris Doya
Ministan Ayyuka da Gidaje na Nijeriya Babatunde Raji Fashola ya bukaci jam’iyyar APC mai mulkin kasar da ta mutunta tsarin karba-karba wajen tsayar da mutumin da zai yi mata takara a zaben shugaban kasa na 2023.
Fashola ya bayyana wannan tsarin na karba-karba a matsayin wata babbar yarjejeniya da iyayen da suka kafa APC suka cimma matsaya a kanta tun gabanin zaben 2015.
Tsokacin Fashola na zuwa ne a yayin da ake takaddama kan ko mulkin Nijeriya zai koma yankin Kudancin kasar da zarar shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa na biyu a 2023.
Gwamnan Ebonyi Dabid Umahi ya sauya sheka daga PDP zuwa APC saboda irin wannan takadda kan tsarin karba-karba tsakanin shiyoyin kasar.
Gwamnan ya ce, ya sauya sheka ne saboda PDP ba ta taba tsayar da dan takarar shugaban kasa daga yankin Kudu maso gabashin kasar ba tun bayan da aka koma mulkin farar hula a 1999.