Khalid Idris Doya" />

2023: Masu Bita-da-kullin Kwace Ragamar Bauchi Daga Gwamna Bala Ba Za Su Yi Nasara Ba – Bibi Dogo

Wani jigo a tafiyar jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Bauchi, Malam Bibi Dogo ya yi bayanin cewa kulle-kullen kwace ragamar mulkin jihar Bauchi da ake yi a hannun gwamna Bala Muhammad ba zai kai ga samun nasara ba lura da dumbin ayyukan raya jihar da yake kan samarwar tun lokacin da ya dale karagar mulkin jihar.
Bibi Dogo wanda ke shaida hakan a jiya Lahadi yayin da ke amsa tambayoyin ‘yan jarida a Bauchi, ya na mai cewa al’umman birni da karkara sun shaidi irin kokari da himmar gwamna Bala don haka da wuya wani ko wasu su iya kaisa kasa balle ma har su iya kayar da shi a babban zaben 2023.
Ya na mai cewa wani taron baya-bayan nan da wasu gungun kungiyoyin siyasa suka shirya da zimmar lalubo bakin zaren hanyoyin da za su bi wajen ganin sun amshi ragamar mulkin jihar a hannun Bala, “Ba za su iya cimma nasara kan hakan ba domin irin dumbin ayyukan raya jiha da karkara da yake samarwa wanda tun bayan dalewarsa kan karagar mulki ya dukufa wajen ganin ya cika alkawuran da ya dauka wa jama’a a lokacin yakin neman zabe.”
Bibi ya kara da cewa ayyukan da gwamna Bala ya samu aiwatarwa a fannin gina kasa da gina rayuwar jama’a hadi da fuskacin kyautata jin dadi da walwalar jama’a kai tsaye sun kai ga matakin inganta rayuwar al’umma wanda masu zabe su na sane da himmar da gwamnan ke yi musu.
Ya ce, “Lokacin da ya dale bisa karagar mulkin jihar, ya maida hankali wajen inganta makarantun da suke fadin jihar kama daga Firamare da sakandari a sassan jihar. Da dan abun da ke akwai a cikin lalitar jihar, ya samu nasarar gina dakunan karatu a gundumomi da ungunnin da suke Bauchi guda 424. Ya kuma gina da yin kwaskwarima wa manyan hanyoyi guda hudu kan kudi naira biliyan biyar a cikin kwaryar garin Bauchi.
“Hanyoyin sun hada da Ibrahim Bako zuwa Maiduguri bye-pass mai nisan kilomita 4.4; Titin da ya tashi daga Sabon Kaura ya nausa kan babban hanyar Jos mai nisan kilomita 6.2; aikin titin rukunin gidajen Yakubun Bauchi mai tsawon kilomita 1.8 da kuma titin kasuwar Muda Lawal mai tsawon kilomita 1. Yayin da kuma wasu hanyoyin ma aka kammalasu a garin Azare da Misau Sade Akuyam kuma akwai wasu hanyoyi sama da 20 da a yanzu haka ake kan gudanar da ayyukansu.”
Jigo a PDP din ya kuma daura da cewa a kokarinsa na ganin an sauya tsarin taswira zuwa matakin kasa da kasa ta fuskacin cigaba mai daurewa, an samu damar kaddamar da aikin gina rukunin gidaje 2,500 a sassan jihar aikin da ya bada damar samar wa matasa sama da 20,000 aikin yi, aikin wanda a cewarsa yanzu haka na kan cigaba da gudana.
Bibi Dogo kuma ce aikin gina gidan gwamnati daidai da tsarin zamani na daga cikin ayyukan da suka zama zakaru kuma da za su kai ga farfadowa da sabunta jihar Bauchi a idon duniya. “Kuma aikin gyaran ruwa na Gubi Dam da yanzu haka gwamnatin ke gudanarwa zai kai ga shawo kan karancin ruwa mai tsafta da jama’a ke fama da shi.”
Masanin harkokin siyasar ya kuma baiwa jam’iyyun adawa shawarar da su daina kwatanta gwamnatin Bala Muhammad da na gwamnonin da suka gabata inda yake cewa, “Bala shine wanda ya kasance na daban a cikinsu ta fuskacin gudanar da aiki tukuru domin talaka da cigaban jihar.
“Da jam’iyyun adawa suka ga ayyukan da yake yi sun kaza yi, wannan dalilin ya sanya su nemo hanyoyin zarge-zarge da neman jefa wa jama’a shakku, to su sani ba za su yi nasara ba domin ayyukan da gwamna ke yi sun nuna asalin wanene shi kuma meye manufarsa ga jihar Bauchi,” a fadinsa.

Exit mobile version