Karamin Ministan Ilimi, Hon. Emeka Nwajiuba, ya yi murabus daga mukaminsa jim-kadan biyo bayan umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na cewa dukkan ‘yan majalisar zartaswa da ke neman mukamai a zaben 2023, su mika takardar murabus dinsu a ranar 16 ga watan Mayu ko kuma kafin ranar 16 ga Mayu, 2022.
shugaban kasar ya bayyana Umarnin ne a ranar Laraba, a karshen taron majalisar zartaswa na kasa (FEC) na mako-mako a Abuja.
Buhari ya yabi ministan akan jajircewarsa wajen yin Murabus din, ganin cewa, Nwajiuba shine Minista na farko da ya bayyana murabus din sa a bainar jama’a.
Nwajiuba dai ya karbi fom din tsayawa takara ne daga jam’iyyar APC mai mulki, domin ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.
A wani yunkuri na kaucewa shari’ar da ka iya kawo cikas ga ‘yan takarar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa, Buhari ya bayar da umarnin cewa dukkan mambobin kwamitin zartaswa (FEC) da ke neman kujerar Siyasa, su mika wasikunsu na yin murabus kafin ranar Litinin 16 ga Watan Mayu, 2022.