Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ya kammala shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar APC zuwa (NNPP).
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Solacebase a ranar Litinin din nan, Malam Shekarau da sauran ‘yan tawagar G-7 na jam’iyyar APC suka fara tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma jagoran jam’iyyar na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
- 2023: Shekarau, Barau Da Kawu Sumaila Na Shirin Ficewa Daga APC zuwa NNPP Kwankwasiyya
- Kotun Koli Ta Ba Tsagin Gwamna Ganduje Nasara Akan Tsagin Su Shekarau
Sanata Ibrahim Shekarau shi ne shugaban tawagar G-7 na jam’iyyar APC ta Kano da ta kunshi Sanatoci 2 da ‘yan majalisar wakilai 5 da sauran jiga-jigan jam’iyyar a jihar.
Majiyar ta ce wannan ya biyo bayan bijirewa zargin da ake wa Gwamna Abdullahi Ganduje na bijirewa umarnin shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu da na shugaban kasa na a bai wa tsofaffin Gwamnoni da Sanatoci masu ci tikitin tsayawa takara ba hamayya.
Ka ga dai abin da muka gano, Ganduje yana wasa da hankalin mutane, su biyu ne ‘yan takara domin ya baiwa Basheer Lado damar sayen fom din tsayawa takarar Sanata, yin hakan ya tabbatarwa hedkwatar kasa tunanin cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Majiyar ta ce rikicin da ba a warware ba a Kano. “A yayin da nake magana da ku G-7, Majalisar Shura (Tsarin Siyasar Shekarau a fadin Kananan Hukumomi 44) da sauran masu ruwa da tsaki za su yi taro a yau Talata, da karfe 10:30 na safe domin kammala shirin,” inji majiyar.