2023: Tinubu Ne Ya Fi Cancantar Zama Shugaban Kasa, Inji Wata Kungiya A Bauchi

Daga Khalid Idris Doya,

Wata kungiya mai suna ‘Disciples of Jagaba ‘Bola Ahmed Tinubu for President 2023’ reshen jihar Bauchi, ta ayyana cikakken goyon bayanta ga jagoran jam’iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu da ya zama shugaban Nijeriya a yayin babban zaben 2023.

Kungiyar tana mai cewa, dukkanin wadanda suke ta shinshina kujerar Shugaban kasa bayan saukar Buhari a jam’iyyar APC babu wani da ya kai Tinubu dacewa da cancanta, don haka ne suka ce Bola ne ya kamata ya zama magajin shugaba Buhari.

A cikin wata sanarwar manema labarai da ko’odintan kungiyar a jihar, Hon. Danjuma Hussaini Sulaiman ya rabar wa ‘yan jarida a Bauchi, ya ce tabbas Tinubu ne yafi cancantar a zaba a matsayin Shugaban kasa a 2023 lura da salon siyasarsa na tafiya da kowa ba tare da nuna banganci ko wariya ba.

Danjuma ya ce, daukar matakin mara wa Bola baya da suka yi, ya biyo bayan irin gogewarsa da kwarewarsa ne da suka duba musamman na zamansa gwamnan Jihar Legas na tsawon shekara takwas da irin cigaba da ya samar.

“Kasancewar Bola Tinubu a matsayin tsohon gwamnan Jihar Legas ya tabbatar da inganta rayuwar al’umma da kuma aiwatar da ayyukan raya jihar. Bisa himmarsa da iya shugabanci nasa, ya tafiyar da gwamnati tare da samar da tagomashi wa kudaden shiga wanda aka samu alfanu sosai.

“Ahmed Bola Tinubu ya kawo cigaba ta kowace fanni a jihar Legas lokacin da ke gwamna. Don haka zaman irinsa a matsayin Shugaban kasa zai kawo cigaba sosai da gyara matsalolin da suke jibge.

“Kari a kan tagomashinsa zai hada kan ‘yan kasa domin baya nuna wariya ko bangaranci. A lokacin da yake gwamna ya baiwa wadanda ba ‘yan asalin jihar Legas ba da dama mukamai a gwamnatinsa. Tabbas irinsa ne suka dace da mulkin Nijeriya.”

Shugaban kungiyar ya kuma kara da cewa, kungiyar ta na da ko’odinetoci a dukkanin kananan hukumomi 20 da suke jihar wadanda suka dukufa yin aiki tukuru domin ganin nasarar Tinubu a 2023.

Exit mobile version