2023: Tsohon Dan Majalisa Ya Nemi Gwamna Bala Ya Amince Da Takarar Shugaban Kasa

Takarar

Daga Khalid Idris Doya,

Tsohon Mambar Majalisar Wakilai ta Tarayya daga Jihar Bauchi, Honorabul Hamisu Mu’azu Shira, ya shaida cewar, yana mai mara baya dari-bisa-dari ga kiran nan da ake ta yi wa gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad na ya fito neman takarar shugaban kasar Nijeriya a babban zaben 2023 da ke tafe.

 

Shira, wanda ya bayyana ta cikin sanarwar da ya fitar wa ‘yan jarida a Bauchi jiya, yana mai shaida cewa tabbas idan Kauran Bauchi ya zama shugaban kasa za a samu natija wajen shawo kan matsalolin da suke addabar kasar na tsaro da na tattalin arziki, gami da zai tabbatar da hadin kan al’umman kasar nan.

 

Yana mai cewa, shi kansa da sauran abokansa tsoffin ‘yan majalisar tarayya da suka fito daga shiyyar arewa maso gabas za su mara wa gwamnan baya sosai wajen ganin ya samu kuri’un ‘yan Nijeriya domin ya zama shugaban kasa a nan gaba.

 

A cewarsa, bisa azama, himma, kokarin gwamna Bala na shimfida ayyukan gina birane da karkara, bada dama wa kowa da kowa domin a dama da su a fannin mulki, muddin ya samu zarafin zama shugaban kasa tabbas zai daura daga wadannan wajen bunkasa cigaban kasa, tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa da inganci ilimi da na aikin gona.

 

“Bisa farin sani da muka yi wa Sanata Bala Muhammad da ingancin jagorancinsa, tabbas kiran da ake masa na ya fito neman shugaban kasa tabbas ya cancanta domin muna da yakinin zai yi abun da al’umman Nijeriya za su yaba sosai. Mu a shiyyar arewa maso gabas ba mu taba yin shugaban kasa ba, don haka yanzu lokaci ne da ya dace mu amince mu mara wa gwamna Bala Muhammad baya dari bisa dari.”

 

Kan tataburzan wacce shiyya ce ta dace ta fitar da shugaban kasa a nan gaba, Shira ya nemi ‘yan kudu da su kasance masu duba abun da ya dace tare da barin Arewa ta cigaba da mulki, lura da shiyyoyin da suka mori siyasa da demoradiyya.

 

Ya misalta kiran gwamnonin kudu na cewa Arewa ta amince musu wajen tsayar da shugaban Nijeriya a 2023 da cewa ya saba wa doka, ya kuma saba wa tsarin demokradiyya wanda ba abun aminta bane.

 

Daga nan, ya nemi ‘yan arewa maso gabas fa da su tashi tsaye wajen yin tuturuwar mara wa gwamna Bala Muhammad baya domin ya zama shugaban kasa a nan gaba, yana mai cewa hakan zai taimaki demoradiyyar kasar nan da cigabanta matuka.

 

Shira, sai ya nemi al’umman Nijeriya da su amince da Bala Muhammad ya fito neman takara a 2023 kana su mara masa baya domin ganin ya bada tasa gudunmawar na shawo kan matsalolin da suke addabar Nijeriya a halin yanzu.

Ya ce, Bala tsohon ma’aikaci ne wanda ya goge sosai da zai iya jagorantar Nijeriya wajen dakile matsalar tsaro, da shawo kan kalubalen da tattalin arziki ke ciki domin ganin an samu gina kasa mai cike da dumbin arziki da ci gaba, uwa-uba ya bayyana Bala da cewa zai yi kokarin dinke kan al’umman Nijeriya.

Exit mobile version