2023: Yaran Tinubu Da Makusantansa Da Ka Iya Taimakon Sa Ko Dankwafar Da Shi

Daga Yusuf Shuaibu,

 

A daidai lokacin da jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Tinubu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben 2023, hakan ya janyo cece-ku-ce a cikin harkokin siyasar kasar nan.

LEADERSHIP Hausa ta duba wasu daga cikin yaran Tinubu da makusansa da ka iya taimakonsa ko dankafar da shi sakamakon bambancin ra’ayin siyasa. Wannan rahoton zai duba wasu daga cikin yaransa da kuma makusantansa wadanda za su iya taimakonsa ko durkwafar da shi a siyasar 2023.

 Lai Mohammed

Wanda shi ne ministan yada labarai da al’adu ya kwashe shekaru masu yawa yana nuna goyon bayansa ga Tinubu. Ya taba zama shugaban ma’aikatan lokacin da Tinubu yake Gwamnan Jihar Legas. Lai Mohammed yad ade yana gudanar da siyasa da jagoran APC. Ana ganin cewa ministan zai goyi bayan Tinubu a wannan zabe.

Babachir Lawal

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya nemi gafarar goyon bayan Tinubu da ya yi a shekarar 2020, na ganin Tinubu ya zama shugaban kasa a 2023.

 

Sanata George Akume

Ministan ayyuka na musamman yana da kyakkyawan alaka da tsohon gwamnan Jihar Lagas. Ya dade yana gudanar da harkokin siyasa da Tinubu tun lokacin da ya sauya sheka zuwa jam’iyyar ACN a 2011 wanda ya zama shugaban barasa rinyaje na majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar.

Gwamna Umar Ganduje

Akwai kyakkyawan alaka a tsakanin Tinubu da Gwamnan Jihar Kano, Umar Ganduje mai dadadden tarihi a cikin harkokin siyasa. Wannan shi ne dalilin da ya sa tsohon gwamnan Jihar Legas yake yawan ziyartar Kano.

 

Farfesa Yemi Osinbajo

Sakamakon yakin neman zaben shugaban kasa a 2023 ya canza sabon salo, ana tsammanin mataimakin shugaban kasa za su kara da tsohon mai gidansa a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC. Tinubu ne ya haskaka Osinbajo a cikin harkokin siyasa, wanda ya ba shi mukamin kwamishinan shari’a a shekarar 1999 zuwa 2007 lokacin da aka rantsar da shi a matsayin gwamnan Jihar Legas.

 

Babatunde Fashola

Tinubu ya taka muhimmiyar raya wajen ganin Babatunde Fashola ya zama gwamnan Jihar Legas, wanda a yanzu shi ne ministan ayyuka da gidaje, inda ko shakka ba za a yi ba zai goyi bayan Tinubu a zaben 2023.

 

Gwamna Kayode Fayemi

Gwamna Fayemi ya kasance dan siyasa kuma yaron Tinubu wanda ya tsaya masa har ya lashe zaben gwamnan Jihar Ekiti a karon farko, amma a yanzu ya nuna sha’awarsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, wanda zai kara da uban gidansa a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC.

 

Rauf Aregbesola

Ministan harkokin cikin gida kuma tsohon gwamnan Jihar Osun yana daya daga cikin makusantan Tinubu a harkokin siyasa. Ya kasance darakta a kungiyar yakin neman zaben Tinubu wanda har ya lashe zaben gwamnan Jihar Legas a shekarar 1999. Sai dai a yanzu sun samu sabani da gwamnan da ya gajeshi, Gboyega Oyetola sakamakon shugabancin jam’iyyar APC a Jihar Osun, ana tunanin ba zai ci gaba da mara wa Tinubu baya ba a 2023, saboda ‘yan’uwantaka da ke tsakanin Tinubu da kuma Oyetola.

Femi Gbajabiamila

Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya nemi afuwa na goyan bayan Asiwaju Bola Tinubu. Shugaban majalisar wakilan wanda aka zabe shi har sau biyar tun a 2003 wanda suke da kyakkyanwan alaka da tsohon gwamnan Jihar Legas. Inda aka yi zargin cewa ya hada mafi yawancin shugabannin kwamitoci a zauren majalisa manyan mukamai wadanda suka fito daga jihohin Legas da Kano domin su mara wa Tinubu baya.

Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan dan asalin Jihar Yobe yana goyan bayan jagoran jam’iyyar APC. Tinubu taimaka wajen tabbatar da ganin sai Lawan ya gaji Abubakar Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawa. An tabbatar da cewa a yanzu lokaci ne da shugaban majalisar dattawan zai biya halarcin da Tinubu ya yi masa.

Obie Omo-Agege

Obie Omo-Agege ya kasance dan majalisan dattawa har karo biyu kuma mataimakin shugaban majalisa wanda ya samu wannan matsayi da taimakon Tinubu. Mafi yawan mutane sun yi Imani da cewa Omo-Agege zai taimaka wa Tinubu wajen tsawa takara a cikin jam’iyyarsa.

Mukhail Adetokunbo Abiru

Sanata Mukhail Adetokunbo Abiru wanda yake wakiltar Legas ta gabas a majalisar kasa. Tinubu ya goya masa baya wajen samun nasara a harkokin siyasarsa, wanda ake tunanin zai yi aiki tukuru wajen ganin ya taimaka wa Tinubu. Abiru yana daya daga cikin ‘yan masalisa guda 10 wadanda suka ziyarci Tinubu a asibitin Landan, a ranar 10 ga watan Satumbar, 2021.

 

Sanata Opeyemi Bamidele

Sanata Opeyemi Bamidele ya kasance dan asalin Jihar Ekiti kuma yana daga cikin ‘yan majalisan da suka ziyarci Tinubu a Ingila. Opeyemi shi ne shugaban kwamitin majalisa da ke kula da harkokin shari’a, kuma ya nuna sha’awar tsawa takarar gwamna a Jihar Ekiti a karkashin jam’iyyar APC. An tabbatar da cewa Opeyemi zai goyi bayan Tinubu ya samu damar tsayawa takara.

Sanata Adeola Solomon

Sanata Adeola Solomon ya kasance shugaban kwamitin majalisa da ke kula da harkokin kudade. Ya ma sani cewa shi yana daga cikin masu giyon bayan Tinubu bisa irin gudummuwar da Tinubu ya shi a cikin harkokin siyasa. Ana tunanin cewa Sanatan zai tabbatar da Tinubu ya samu damar lashe zaben shugaban kasa.

Sanata Adelere Oriolowo

Sanata Adelere Adeyemi Oriolowo wanda yake wakiltar Osun ta yamma a majalisar dattawa, ya kasance dan-gani- kashe ni na Tinubu ne. Dan majalisan sun gudanar da ayyuka da dama da shi da Tinubu kuma yana daga cikin wadanda suka ziyarce shi a asibitin Landan.

Sanata Mohammed Sani Musa

Sanata Musa wanda ke wakiltar Neja ta gabas a majalisa dattawa, wanda yake neman shugabancin jam’iyyar APC. Musa yana daga cikin ‘yan majalisan da suka nuna amincewarsu da Tinubu tun yana asibitin Landan. An tabbatar da cewa yana goyon bayan takarar Tinubu na tsawyawa takarar shugabancin kasa a 2023.

James Faleke

James Faleke dan majalisar wakilai ne da ke wakiltar mazabar Ikeja a zauren majalisar wakilai. James Faleke yana daya daga cikin wadanda suka yi wa Tinubu yakin neman zabe a zauren majalisar wakilai. Faleke ya bayyana cewa Tinubu shi ne ya fi dacewa a ba shi tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 karkashin jam’iyyar APC.

Lado Suleja

Dan majalisa ne da ke wakiltar mazabar Suleja/Tafa/Gurara a Jihar Neja, Abubarkar Lado Suleja yana daya daga cikin masoya Tinubu a zauren majalisar wakilai. Lado ya kasance baya boye goyan bayan takarar Tinubu, inda ya taba kiran Tinubu shugaban kasa a wajen taro. Lado ya bayyana cewa Tinubu ne ya kamata ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shehu Koko

Dan wajalisar wakilai ne da yake wakiltar mazabar Koko/Besse a Jihar Kebbi a zauren majalisa kuma shi ne shugaban kwamitin majalisa da ke kula da sojojin sama wanda ya kasance yana daga cikin masu goyon bayan Tinubu.

 Muhammed Garba Datti

Shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin wasanni, Hon Muhammad Garba Datti ya kasance masoyin Tinubu. A mafi yawan taruka yana nuna goyan bayansa ga jigon jam’iyyar APC. Wannan ne ya sa yake kalubalantar wasu ‘yan majalisa da su goyi bayan Tinubu.

 

Alhassan Ado-Doguwa

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai yana daya daga cikin wakilan arewa da suka ziyarci Tinubu a Landan. Ko da yake mafi yawancin ‘yan majalisan wakilai daga Jihar Kano na goyon bayan Tinubu na tsayawa takara a 2023. Doguwa ya bayyana cewa Tinubu ya kasance dan siyasa mai wahalar samun irinsa.

Dakta Femi Hamzat

Dakta Femi Hamzat a yanzu haka shi ne mataimakin gwamnan Jihar Legas. Hamzat ya kasance kwamishinan kimiyya da fasaha a lokacin da Tinubu yake matsayin gwamnan Jihar Legas a shekarar 2005. A shekarar 2011, an nada Dakta Hamzat a matsayin kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa.

 

 

Mista Tunji Bello

Mista Tunji Bello, a yanzu haka shi kwamishinan muhalli da ruwan sha na Jihar Legas. Yana daya daga cikin mutanen da Tinubu ya daya kafarsu a cikin harkokin siyasa, domin ya kasance mai rike da mukami tun lokacin Tinubu a shekarar 2003 har zuwa yau.

 Sanata Musiliu Obanikoro

Tsohon karamin ministan tsaro, Sanata Musiliu Obanikoro ya kasance masoyin Tinubu da ke neman ganin ya zama shugaban kasa a zaben 2023. Ya kasance kwamishinan al’adu na Jihar Legas a shekarar 1999 lokacin Tinubu. An dai zabi Musiliu Obanikoro a matsayin dan majalisar dattawa mai wakiltar Legas ta tsakiya a zaben 2003 karkashin jam’iyyar AD da Asiwaju Tinubu yake jagoranta.

Demola Seriki

Demola Seriki ya kasance karamin ministan tsaro a tsakanin shekarar 2008 da 2009. A ko da yaushe yana kalubalantar duk wani dan takara da ya yi hamayya da Asiwaju Tinubu.

 

Rt. Hon. Mudashiru Obasa

Rt. Hon. Obasa, shugaban majalisar dokokin Jihar Legas. Obasa ya kasance mai goyan bayan jigon jam’iyyar APC. Ya kasance dan gani kashinin Tinubu a siyasance.

Exit mobile version