Ministan kwadago, Dakta Chris Ngige, ya ce, sai ya fara tuntubar Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, da neman shawararsa da kuma tuntubar al’umar mazabarsa gabanin ya dauki matakin ajiye mukaminsa na minista a tarayyar Nijeriya.
Ministan wanda ke tofa albarkacin bakinsa kan umarnin da shugaban Buhari ya bai wa Ministocinsa na cewa duk mai sha’awar yin takara a zaben 2023 da ke tafe ya ajiye mukaminsa kafin ranar 16 ga watan Mayun 2023.
- 2023: Duk Jam’iyyar Da Ta Bai Wa Arewa Takarar Shugaban Kasa Za Ta Fadi – Ngige
- Fetur Da Lantarki: Babu Sauran Kudaden Tallafi – Ngige
Ngige, wanda ke wannan maganar bayan zaman Majalisar zartaswar Nijeriya da ya gudana a ranar Laraba a Abuja, ya ce, Buhari ya bai wa wadanda suke neman karin haske damar nema idam suna son hakan daga wajensa, saboda haka Ngige ya ce zai gana da Buhari kan wannan batun.
Ya ce, “Ba zan dauki mataki yanzu ba saboda shugaba Buhari ya ce duk mai neman karin bayani ko haske yana iya nemansa. Don haka zan nemi shawararsa tare da al’umar mazabata a jihar Anambra saboda ina rike da mukamin gwamnati da al’umata.”