2025 UTME: Cibiyoyin Zana Jarabawar 11 Na Fuskantar Barazanar Dakatarwa - JAMB
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2025 UTME: Cibiyoyin Zana Jarabawar 11 Na Fuskantar Barazanar Dakatarwa – JAMB

bySulaiman
4 months ago
JAMB

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta bayar da shawarar yanke hukunci mai tsauri kan cibiyoyi 11 da ake zana jarrabawar ta kwamfuta acikinsu (CBT) da masu rajistar daliban biyo bayan samunsu da kura-kurai wajen tantance masu zana jarabawar ta 2025 (UTME).

Shugaban Hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana haka bayan wani zaman tattaunawa da wasu masu ruwa da tsaki da kuma wadanda ake zargin a ranar Talata a Abuja.

  • Xi Ya Gabatar Da Muhimmin Jawabi A Taron Koli Na Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya Karo Na Biyu
  • Daga Taklimakan Zuwa Sahara: Karin Abubuwan Al’ajabi Na Faruwa Bisa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Yaki Da Kwararar Hamada

Oloyede ya ce matakan da har yanzu ke bukatar amincewar Ministan Ilimi, Dokta Maruf Tunji Alausa, an tanade su ne da nufin kare martabar tsarin jarabawar.

Ga cibiyoyin CBT, Oloyede ya ce dole ne a gargadi wadanda ke da hannu sannan a nemi su sanya hannu kan takardar yarjejeniya. Kuma bayan yarjejeniyar, za a kuma buƙaci su ba da shaidar horar da masu rajistar daliban.

Da yake karin haske kan shawarwarin, Oloyede ya ce hukumar ba za ta yi la’akari da duk wani uzuri ba daga cibiyoyin da abin ya shafa a nan gaba ba, duk da ikirarin da suke yi na rashin sani, don haka akwai bukatar su samu horon da ya dace a jami’o’in gwamnatin tarayya da ke kusa da su kafin JAMB ta kara amincewa da su.

Cibiyoyin CBT da abin ya shafa da aka gayyata taron sun hada da Misau Emirate ICT Centre, Misau, Bauchi, Ijaw National Academy, Kiama, Bayelsa, Directorate of ICT Nigerian Army University, Biu, Gombe, Emerald IT Academy Limited, Benin, Tigh Technologies, Sascon International School, Maitama, Abuja, Jicoras CBT Centre, Babura, Jigawa da Huntsville Technology Limited, Anthony, Legas

Sauran sun hada da Jolas College CBT Centre, Obalende, Lagos, Abdul Ocean Weath CBT Centre, Ibadan, Oyo State, National Open University of Nigeria (NOUN), Wase, Filato da Consulate Salle D’Examen CBT Centre, daura da Jonny Lane/Navy Barrack Agip Estate, Jihar Ribas.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Sin Ta Fara Aiwatar Da Matakin Soke Haraji Kan Kayayyakin Kasashen Afirka 53

Sin Ta Fara Aiwatar Da Matakin Soke Haraji Kan Kayayyakin Kasashen Afirka 53

LABARAI MASU NASABA

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version