2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

byYusuf Shuaibu and Sulaiman
4 months ago
PDP

Majiyoyi sun bayyana cewa wasu daga cikin gwamnonin jami’yyar PDP na shan matsinlamba don su sauya sheka zuwa APC. Majiyoyin sun tabbatar da cewa fadar shugaban kasa da jam’iyyar APC suna kara matsinlamba ga wasu gwamnonin PDP domin sauya sheka.

Kazalika, majiyoyin sun shaida cewa wasu daga cikin gwamnonin adawa suna cikin rudani sakamakon rikicin da ke cikin PDP, wanda da yawa daga cikinsu ke fargabar zai raunana damar samun sabon zangon mulkinsu na biyu.

  • Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe
  • Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

Matsinlambar na tilasta musu sauya sheka yana zuwa ne a yayin da PDP ke ci gaba da fuskantar rikice-rikice da suka haifar da rabuwar kawuna a jam’iyyar a halin yanzu.

Haka kuma majiyoyin sun bayyana cewa gwamnonin PDP suna cikin damuwa game da halin da aka kafa a Jihar Filato, inda kotuna suka tsige ‘yan majalisar jiha na PDP da wasu ‘yan majalisun tarayya saboda rikice-rikicen cikin gida da ba a warware ba a matakin kasa. Abun tsoron shi ne, idan rikicin ya ci gaba da tafiya a haka, kowanne dan takara da PDP ta zaba, ciki har da dan takarar gwamnonin da ke neman tazarce, kotu na iya kwace zaben cikin Ruwan sanyi.

Rahotannin sun bayyana cewa duk da shaharar gwamnan Umo Eno na Jihar Akwa Ibom, yana fuskantar wani kalubale daga wanda ya gada, Udom Emmanuel, wanda ke rike da karfin ikon tsarin siyasar PDP a cikin jihar.

Wasu sahihin rahotannin daga cikin gwamnatin sun shaida cewa Gwamna Eno ba zai iya sauya sheka zuwa APC ba tare da amincewar Emmanuel ba, domin yin hakan na iya jawo masa asarar goyon bayan mambobin majalisun kasa da na jihar, ciki har da sauran muhimman masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

An kuma tattaro cewa wani bangare na shirin fadar shugaban kasa shi ne, dukkan jihohin Kudu Maso Gabas su kasance na APC. Gwamnonin kamar Hope Uzodimma su ne kan gaban wajen yin matsinlamba ga Gwamnan Peter Mbah na Jihar Inugu, Aled Oti na Jihar Abiya da Chukwuma Soludo na Jihar Anambra don su sauya sheka zuwa APC. Duk da haka, rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan Inugu bai bayar da cikakken amsa kan lamarin ba, Soludo ba ya son shiga APC saboda yana ganin zai iya samun nasara a jam’iyyarsa ta APGA.

A Jihar Jihar Zamfara kuwa, an gano cewa fadar shugaban kasa ta nuna sha’awarta na shigo da gwamnan cikin jam’iyyar APC. Duk da haka, daya daga cikin matsalolin shi ne, akwai wadanda ba sa son lamarin ya tabbata kamar karamin ministan tsaro, Bello Matawlale.

A cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a ‘yan kwanakin nan kan shirin komawa APC, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce a halin yanzu yana nan a cikin PDP.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Next Post
Adawa

Yadda Rarrabuwar Kawunan Jam'iyyu Zai Iya Sauya Alkiblar Zaben 2027

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version