Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich dake kasar Jamus ta doke abokiyar hamayyarta wato kungiyar Borussia Dortmund daci 3-1 a wasan mako na 31 ranar Asabar ta kuma lashe Bundesliga na bana.
Kungiyar ta Jamus ta ci kwallayen nata ne ta hannun Serge Gnabry da Robert Lewandowski da kuma Jamal Musiala yayin da ita kuwa Dortmund ta zare daya ta hannun Emre Can a bugun daga kai sai mai tsaron raga. Kungiyar da Julian Nagelsmann ke jan ragama ta ci kofi na 10 a jere tun daga kakar wasa ta 2012 zuwa 2013 ta kuma lashe na bana na 32 jumulla da tazarar maki 12, saura wasa uku a kammala kakar nan.
Bayern ta yi wasa tara a jere ba tare da rashin nasara ba, kuma karawa hudu aka doke ta a kakar nan har ila yau dan wasa Robert Lewandowski ne kashin bayan kungiyar, wanda ya zura kwallo 33 a raga a kakar nan, sai dai a bara guda 44 ya zazzaga, sannan ya kafa tarihin yawan cin kwallaye a gasar ta Bundesliga.