Sulaiman Bala Idris" />

24 Ga Oktoba Kotu Za Ta Yi Hukuncin Shari’ar Atiku Da BCO

Wata babbar kotu da ke zama a babban birnin tarayya, Abuja ta ayyana ranar 24 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta yi hukunci kan karar da kungiyar BCO ta shigar inda ta ke neman diyyar naira miliyan 40 daga wurin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Kungiyar na neman wannan diyya ne bisa zargin Alhaji Atikun da cin mutuncin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A karar wacce aka shigar ranar 22 ga watan Janairun 2019, Kungiyar BCO ta sanar da kotu cewa Atiku ya ci mutuncin Shugaban Kasa Buhari ta hanyar ikirarin cewa Shugaban Kasan da wasu daga cikin iyalansa suna da hannun jari a kamfanin 9mobile, da kuma bankin Keystone.

A takardar rantsuwar shaida, wanda Daraktan sadarwa da tsare-tsaren Kungiyar BCO, Mallam Gidado Ibrahim ya yi, ya shaida cewa Atiku da jami’in yada labaransa sun yi amfani da salon cin mutunci don bata sunan Shugaban Kasa Buhari, wanda har daukar nauyin wallafawa a wasu jaridu suka yi.

Kungiyar BCO na neman ta yi hukunci kan wanda take kara na farko, wato Phrank Shaibu, a madadin wanda a ke kara na biyu wato Atiku bisa daukar nauyin cin zarafi da keta mutuncin mai kara na farko, wato Shugaban Kasa Buhari. Kungiyar ta BCO ta shigar da kara ne a madadin wanda ya shigar da kara.

Haka kuma kungiyar BCO na neman kotun da ta tursasawa wanda a ke kara da ya biya masu kara diyyar naira miliyan 30 saboda wahalhalun shari’a da suka sha. Haka kuma masu karar sun bukaci kotu ta tilastawa wanda a ke kara ya biya wata diyyar ta naira miliyan 10 domin bata suna da wanda a ke karar ya janyowa masu kara, musamman ma mai kara na farko wanda babban mutum ne, kuma dan takarar shugaban kasa.

Sai dai a nashi martanin, Atiku ya nemi kotun da ta kori shari’ar, duk da shi ma ya bukaci shugaban kasa Buhari da ya biya shi diyyar naira biliyan 200. Wannan na kumshe ne a takardar martanin da Atikun ya mayar ga karar da BCO ta shigar da shi.

Sai dai bayan sauraron dukkan bangarorin biyu a jiya, kotu ta sa ranar 24 ga watan Oktoba domin yanke hukunci a kan shari’ar.

Exit mobile version