Kansar Yara: Wata Annoba Da Ba A Sa Ta A Lissafi

Yayin da gamnatin tarayya ta fi mayar da hanakalinta akan cututtukan da suke yaduwa, cutar sankara da kuma asu cututtuika wadanda ba su saurin yaduwa, sune suka fi saurin kashe Yara kanana, wadanda suke mutuwa tun suna ‘yan kanana, irin haka ya kawo cikas akan wadanda ake sa ran nan gaba sunezasu ja ragamar kasar.

Sankara wani suna ne wanda ake amfani da shi idan ana son ayi maganar cututtuka daban daban, ta yadda wasu sinadarai na jiki suke samun raguwar yadda halittar take, ko kuma ta yi aikin dabai kamata ba,ko  rayuwa irin w bata dace ba. Wannan ba cuta daya bace dominkuwa da akwai sunaye n sankara daban–daban, abin da kesa wani sashe na jikin mutum ya girma har abin ya wuce ka’ida.

Ita sankara ata cuta ce da wurin da ta kama yake kunburi har ya iya shafar wasu sassa, wannan kuma yana faruwa ne ta hanyar jini, abin da ya kamata a kira su shi ne sojoji, irin wannan cutar wani lokaci akan kasance ne, bata damuwar anda yake da ita, amma kuma idan ba ‘a dauki mataki ba, tana iya samar da matsala.

Bincike ya nuna a karnin da ya gabata yawan al’ummar Nijeriya idan ka yi la’akari da yadda tattalin arzikin kasa yake , ana iya cewar kusan duk kamar an fi kudaden da ke shigowa yawa, domin da akwai ayyukan da ba’a samarwa da kuma na more rayuwa. Ana Yara wadanda basu kai shekaru goma sha biyar ba, wadanda sune kashi 45 na yawan jama’ar Nijeriya.

Majalisar dinkin duniya ta kiyasta Yara 30,000 an duba  su an kuma gano suna da cutar Sankara duk shekara, wani abu kuma shi ne kashi 80 cikin dari nasu daga kasashen masu karamin karfi suke, kamar Nijeriya. Gaba daya a duniya ana da Yara wadanda suka kamu da sankara 160,000 da suka kamu da ani sac=bon samfuri na cutar Sankara, ana kuma rasa rayukan Yara ‘yan kasa da shekaru 15 , dubu casa’in duk shekara.

Kamar sankarar babban mutum ita ma ta Yara tana da nata matsalar, akwai cutar sankara daban daban, wadda zata ya yin tasiri a jikin Yaro, duk kuma yadda take rayuwa jikin babban mutum , hakanan take yi a jikin Yaro. Kamar ma shi babban ana iya samun cakudewar al’amura.

Yawan mutane basu san cewar Yara ma suna iya kamua da cutar Sankara, suma suna da tasu sankara fiye da manya, amma kuma maganin duk daya ne, wanda ake kira da suna chemothraphy, ko kum ayi fida, da kuma at6a kulaata musamman. Akwai sankara ta ido, da kuma kashi

Yawancin cututtukan sankara da suka sha bamban sun kuma hada da Leukemia wadda sankara ce ta jini, Kwakwalwa, da kuma kokon kai, sankara wadda take ana samunta a kirji da kuma cikin ciki.  A kwai kuma sankarar Wilms wadda ta shafi koda ne. Wani kwararre akan cutar sankara wanda kuma yake da kungiya maisuna Dorcas Foundation Dr Adedayo Joseph wanda shi ne shugaban kungiyar wanda ya jagoranci yadda ake tara kudade, saboda ayi magani cututtukan sankara wadanda aka gano su da sauri, ya ce, abin bakinciki har zuwa yanzu ba ,a san  yadda ake kamuwa da cutar sankarar Yara ba, amma dai ana danganta ta, da ta kayoyin haihuwa abin da ba wanda ya isa ya dauki wani mataki akai.

Akwai cututtukan sankaradaban daban yawancinsu ba’a san dalilin da ake kamuwa dasu ba, wasu cututtukan sankara ana dangantasu da biral ko kuma yadda mutum ya kusanci wani abin da zai iya cutarwa, ko mahaifi ko kuma shi Yaron. Ko kumawasu sinadarai kamar Benzene, Maganar gaskiya sankarar Yara ana kamua da ita ne,  a dalilin ta mahaifa al’amarin ba wanda zai iya  wani abu. Har yanzu kuma masu bincike sun shaida haka.

Rage matsalolin da ake fuskanta dangane da cutar sankarar Yara abu ne mai wuya, ba kamar sankarar manya ba, sankarar da aka danganta ta, da irin abincin da ake ci, yadda mutum yake rayuwa, ita sanakarar Yara ba, a iya maganinta cikin sauki.

Ta ce a matsayin ta na Uwa ta tuna da yadda maganin sankarar Yara da ake kashe kudade masu yawa, wanda har yanzu abin shi ne ya kasance babbar matsala, ta hanyar magani ita cutar kansa an iya rasa rayuwa, bugu da kari kuma cutar ana kashe kudi masu yawa, wajen neman magani. Ana iya kashe Naira milyan 2 tun daga binciken gano ita cutar da kuma magani, da kuma yadda za, a trairayi Yaro bayan ya samu sauki. Yazuwa yanzu Dorcas Foundation ya samar da kudade na yi ma Yara goma magani, wannan abin ayi godiya ne saboda mutane da yaw aba zasu iya haka banan ba.

Yanzu shi asusun ya mayar da hankalin shi ne a kan taimakawa akanal’amarin da ya shafi sankarar Yara, amma kuma ba zasu fara ba, sai sun tabbatarda suna isassun kudaden da za, a biya har zuwa karshen samun sauki. Ta ce, asusun bai dade da bude wani shiri na maganar sankarar da ke faraw tun daga kananan shekaru na Yara, wanda wani littafi ne, an kuma far fito da na farko daga cikin wadanda suke bayani dangane da sankarar Yara. Gidauniyar ta yi niyar fassara littatafan zua harsunan gargajiya, a Nijeriya, hakana kuma za.a cigaba da fitar da littattafai masu yawa,domin  a fadakar da Iyalai, marasa lafiya, da kuma kwararru masu kula da lafiya, dangane da cutar sankara ta Yara.

Farfesa Remi Adekingbe wanda shi ma wani kwararre ne a Asibitin koyarwa na jami’ar jihar Lagos, kira ya yi da a rika kokarin bincike da kuma gano ita cutar, da kuma maganin da ya dace da ita. Adekingbe ya yi kira da da gwamnatoci da kuma mutane masu zaman kansu, da su hada kai domin a samu ceto rayuwar mutane adanda suka kamu da cutar, saboda yadda ake kula da marasa lafiyan da kuma kudaden magunguna abin nada tsada

Cutar sanakar ba ruwanta da kowa idan mahaifiya ta lura dawani abin da bata gane ba, ya kamata ta samu sanar da asibiti bada dadewa ba, lura da kuma bada magani ana kashe kudade masu yawa, a Nijeriya yanzu ana da mashina guda bakwai da ake amfani dasu akan maganain cutar sankara. Bayan kuma ana da marasa lafiya 200. Marasa lafiya ba zasu iya biyan kudin maganin da kansu, don haka suna bukatar taimako daga kungiyoyi masu zaman kansu har ma da gwamnati.

Kamar yadda Hukumar lafiya ta duniya ta ce dukkan ire iren cututtukan sankara suna kasancewa ne a sanadiyar yadda wasu sassa ko wani sashe na jikin mutum zai canza daga yadda yake tun asali. Hara bin ya kai ga zai kai ga addabar mai dauke da cutar.

Hukumar lafiya ta ce shi canjin da ake samu najikin mutum wani sakamako ne na hulda da ake yi tsakanin kwayoyin halittar dan Adam da kuma wasu abubuwa uku na waje da suka hada da yadda muhalli yake, hasken rana, da kuma hayakin taba da akai kuma abincin da ya gurbata, sai kuma ruan sha shi ma wanda bai da tsabta, ga kuma wata cuta daga kwayoyin cuta kamar su biruses, bacteria, ko kuma parasites.

Hukumar lafiya ta duniy ta hanyar mai yi mata bincike wani kamfanin bincike na kasa da kasa, a kan   cutar sankara (IARC) sun tsaya kan abaubuwan da suka sa cutar sankara. Tsufa ya na daga cikin abubuan da kan taimakawa ita cutar yaduwa, abin yana da alka ne da shekaru wannankuma ya kasance haka ne saboda yadda jikin yake ato bai karuwa wani lokaci sai raguwa.

Hakanan ita Hukumar lafiyar ta yadda cewar shan Taba, Giya da kuma cin abinci maras kyau, da kumarashin motsa jiki, wanda shi ne babban dalili, a duk fadin duniya, hakanan ma asu abubuwa hudu wadanda suma sun hada da cututtukan da basu da saurin yaduwa, sai kuma cututtukan da zasu iya samuwa, a dalilin cutar sankara, ana samunirin cutar a wurin  masu kudi na tsaka- tsaki da kuma na kasa-kasa wato kasashe, abin ya danganta ne akan tattalin arzikinsu.

Ana iya rage kamua dacutar sankaraidan ka gano ita cutar da wuri aka kuma samar da magani, idan ka gano ta wuri cutar zata iya yin kasa sosai idan anakula d abada magani, anaiya samun tsira daga abubuan da iya kawo karshen rayuwar mai cutar.

 

Exit mobile version