2019: Shekara  Ce Da Talaka Zai Shirin Zaben Wanda Zai Tallafa Ma Sa

Tun kafin a tsunduma wannan sabuwar shekara ta 2018,ma su tsokaci kan al;amurran yau da kullun za ka ji suna bayar da ra’ayoyinsa masu karo da juna ,wato wasu na cewar,ana tsalle ne inda ake dira ko kuma ana dira inda ake tsalle daga shekara ta 2015 zuwa wannan shekara ta 2018 da muke ciki. Wadannan batutuwa suke sa ake sa zannin cewar an ya wadanda ke madafun iko za su tsallake siradi a shekara ta 2019, ko kuma ko za a tashi daga sak ne zuwa cancanta?

Wakilinmu BALARABE ABDULLAHI ya sami damar zantawa da wani fitaccen dan siyasa kuma shugaban jam’iyyar ADP a jihar Kebbi ALHAJI DANTANI DIO, inda ya yi tsokaci kan sabuwar shekara  ta 2018,da kuma yadda ya ce babu ko shakka,al’ummar Nijeriya  za su nuna an fa yi walkiya,wadanda suka make an gansu,ya ce talakawan Nijeriya za su tabbatar da haka a shekara ta 2019.

Ga  dai yadda wannan tattaunawa ta kasance da Alhaji Dantani Dio

Ya ka kalli wannan sabuwar shekara ta 2018 da aka shiga?

Da farko wajibi ne mu gode wa Allah da ya sa mu cikin wadanda suka ga wannan shekara ta 2018, domin babu shakka Allah bai ba wasu damar ganin wannan shekara ba. Amma a siyasance, mu ‘yan Nijeriya babu wani abu guda daya da za mu ce za mu yi godiya ga wadanda muka yi amfani da lokacinmu da karfinmu da karfinmu da tunaninmu da iliminmu muka zabe su, har zuwa yau babu wani abin a zo a gani tukuna.

 

Gaba daya bau wani abu da kake ganin an sami nasara a kansa ko a kansu daga shekara ta 2015 zuwa wannan shekara ta 2018?

Wadanne nasarori aka samu, sai dai sun samu a cikin yunwa da kuma wahalhalun da ba za su kidayu ba. Domin dan’uwana talakan Nijeriya abin da ya yi tunani shi ne,bayan ya zabi jam’iyyar APC  zai je asibiti ya sami magani kyauta ko da ‘yan kudi kankani ba,  ba zai kuma sami rayuwa mai inganci tare da iyalansa, amma sai aka wayi gari rayuwa ta Zama mai tsada ta ko wane bangare na dan Nijeriya.

 

Amma fa ka tuna a shekara ta 2015, kana sahun gaba, na yakin ganin jam’iyyar APC  ta sami nasara, ba a jihar ka ta Kebbi ba, ba a bin mamaki ba ne wadannan batutuwa su fito a bakinka?

Baa bin mamaki ba ne,mu tun farko,mun rungumi jam’iyyar APC ne da tunanin za a gyara abubuwa da dama da jam’iyyar PDP ta bata,sai mu ka wayi gari hakan bai tabbata ba,wato mu ka sami akasin haka,kuma duk dan Nijeriya ya san wannan batu haka take,babu canji ko kadan.

Wannan ne ya sa dole mu fito mu bayyana wa ‘yan’uwanmu talakawa da su ne suka dora gwamnatin APC a jihohi ko kuma a tarayya cewar su yi hakuri, zaton abin kirki ya sa muka yi ruwa muka yi tsaki kafin

shekara ta 2015,amma sai batu ya canza,to wajibi ne a shekara ta 2019, talakawam Nijeriya su yi niyya da kuma  aiwatar da zaben wadanda za su warware ma su matsalolin da aka sa su a ciki, wato matsalolin da na ambata a baya.

Wato abin da na ke nufi shi ne, mu zabi wanda zai share wa talaka hawayensa,kamar man fetur ya  dawo kamar yadda yake kafin jam’iyyar APC ta fara mulki, kuma mutum ya je kasuwa ya sayi buhun shinkafa Naira dubu bakwai ko kuma takwas, wato yadda farashin yake kafin shekara ta 2015.

 

Ire-iren wadannan batutuwa ne ku ke fadi ku ‘yan siyasa kafin zabubbukan da suka gabata,an ya bas hi ake kira siyasa ba,wato kalmomin da ake kwashe kafar mai zade?

Ai ban bayyana ma ka dan takara nab a a jiha ko a sauran mukamai,cewa na yi talakawa ‘yan uwana,mun san mutumin kirki,mun kuma san akasin mutumin kirki,domin an sha mu amma fa ba mu warke ba,domin ko da za mu warke, sai mun zabi mutumin kirki a zaben 2019,in mun yi haka shi ne za mu ce an sha mu mun warke. Ni da al’ummar Nijeriya za su yadda da ni,duk wanda aka zabe shi sau0 daya,a aje shi gefe guda, a sa wani, amma in harm un tabbatar mutum ya yi abin kirki,to mu yi kasada mu ba shi dama ta biyu, in kuma ya yi canji irin na APC,sai mu ce mun ga darasin da za mu dauki matakai a zabe na gaba a kansa.

 

Mutumin kirki a siyasa ba kamar kwarya b ace da za ka kwankwasa ka gane mai kyau kafin zabe,ya za a gane nagari kafin zabe dab a zai yin a hawainiya ba?

Da farko zan gaya ma ka duk wanda ya yi wayau ko yak e da wayau a shekara ta 1983,ya san abin day a faru a wancan shekara,kuma shi ne yak e faruwa a yau,ba a wannan shekara ba,ko kuma in ce tun daga 2015 zuwa wannan sabuwar shekara ta 2018 da mu ka shiga.Amma saboda mantuwa na dan Nijeriya,,mun san karan can a shekara ta 1983 ta na kiyashi a jikinta sai mu ka sake dauko ta a shekara ta 2015,to ka ga darasin da na bayyana ma ka bayyana ma ka a baya a yanzu ka gane karatun kila.Kuma shekara ta 1983,duk gidan da ake shan garin rogo,gidan ma su arziki ne,to yanzu kan mage yaw aye,Allah ya kai mu 2019.

 

In har ba a sami canjin da ke son talakan Nijeiya ya kara samar wa bai samu ba,wani tunani ka ke yi wa dimkuradiyyar Nijeriya bayan shekara ta 2019?

Allah ya sa ba za mu ga haka ba,amma in haka ta faru,to al’ummar jamhuriyyar Nijar za su sami ‘yan gudun hijira daga Nijeriya kila ma har Kamaru da kuma Kasar Cadi.Domin gwamnati ta cire tallafi a man fetur,shi ya sa mu ke ciki matsalar man fetur,an cire tallafi a aikin Hajji,kowa ya san kudin aikin Hajji kafin 2015,kuma an san yadda aka biya a 2017.tsadar abinci ta dabaibaye kowa,wasu wadanda aka zaba korar wadanda suka zabe su suke yi,wasu tantancewar karya suke yi,wasu tallafawa manoma na karya suke yi,in ka lura,wannan mulki talaka da ya zabe suka sa shi a gaba,to na ce ma ka za mu yi karatun-ta-natsu a shekara ta 2019 in Allah ya kai mu.

 

Ka na ganin talakawan Nijeriya za su karbi wannan shawarar da ka bayar?

To ni dai na yi abin da wani mawaki ya ce,’’in za ka fadi fadi Gaskiya, komi ta ja ma ka ka biya,ya kara da cewar,’’in an fadi ma ku Kun yi dariya, dariyarku ta zama kuka a gaba’’Domin duk abin da na fadi na fadi ne bisa sanin abubuwan da suka faru a baya da kuma sanin abubuwan da suke faruwa a yau a gwamnatin da muka zaba da tunanin za ta warware ma na matsalolin da muke ciki, sai aka sami akasin haka,wanda duka wanda zai fadi gaskiya ya san haka.

 

A baya fa in ka tuna duk jam’iyyar da ta ke da gwamnati, in an yi zabe, ita ke lashe kujerun zaben, an ya ka na jin hakan ba zai faru a 2019 ba?

Babu ko shakka an yi haka a zabubbukan baya,bamma a zaben 2019 ba zai yi wu ba, domin fa a baya na ce maka kan mage ya waye, kowa idonsa na bude, ka tuna mafiya yawan wadanda ke majilisu jihad a kuma tarayya da gwamnoni kurar da ta murda ce ta kai su inda suke a yau, to a 2019,babu batun sak sai dai cancanta kawai,Allah dai ya kai mu.

 

Ka na ganin jam’iyyarku ta ADP ta yi nadain da za su ta warware matsalolin da ka dade ka na bayyanawa ?

Ina son ka fahimta,duk wadanda ke ADP irinmu ne ma su son canji na hakika da talakan Nijeriya zai sakata yaw ala,duk abin d azan fadi,tabbas dinsa sai mun kafa mulki a 2019 ‘yanNijeriya za su gane sun yi zaben wadanda ke tunaninsu kafin zabe da kuma bayan zabe.

 

Exit mobile version