Connect with us

TATTAUNAWA

Ba Matsalar Da Murabus Din Nuhu GiDaDo Za Ta Haifar Mana -Kwamared Sabo

Published

on

KWAMARED SABO MUHAMMAD Shi ne babban mai tallafa wa gwamnan jihar Bauchi kan ilimi da faDakar da jama’a a hirarsa da LEADERSHIP A Yau Asabar ya bayyana cewar murabus Din da mataimakin gwamnan Injiniya Nuhu GiDaDo da ya yi a kwanan nan babu wata barazana da kuma tarnaKi da hakan zai jawo musu, ya bayanin cewar mataimakin gwamnan ya ajiye aiki ne don Kashin-kansa ba wai don ana Kin tafiya da shi a fagen gudanar da gwamnati ba, ya kuma shaida cewar a shirye suke su karBi dukkan abin da tsohon mataimakin gwamnan zai bijiro da shi. Ga hirar ta su ta kasance da wakilin namu KHALID IDRIS DOYA:

 

 

Masu karatunmu za so ka fara gabatar da kanka.

Sunana Kwamared Sabo Muhammad babban mai tallafa wa gwamnan jihar Bauchi kan ilimi da faDakar da jama’a.

 

Me za ka ce kan murabus Din da mataimakin gwamnan jihar Bauchi Nuhu GiDaDo ya yi?

Na farko dai shi tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi Nuhu GiDaDo, mun ga takardarsa wadda ya miKa wa mai girma gwamnan jihar Bauchi a ranar 16 ga watan Mayu, 2018. Kuma abin da muka fahimta ya ajiye wannan muKamin nasa ne a bisa Kashin kansa, kuma a tsarin tafiyar gwamna muna yi masa fatan alheri, kamar yadda shi ma a cikin takardar ta sa ya nuna zai ci gaba da kallon gwamnan a matsayin mai gidansa, a matsayin mutumin da yake da kima a wajensa. Bayan haka mu a gwamnatance muna yi masa fatan alheri a dukkan abubuwan da zai sa a gaba a cikin hidimominsa na rayuwa. A matsayinmu na magoya baya da masoyan gwamnan Bauchi muna ci gaba da neman Karin goyon baya da fahimta na jama’a domin ya samu zarafin gudanar alKawuran da ya Dauka a lokacin yaKin neman zaBe.

 

Ba ka ganin irin wanan ajiye aiki da muKarraban gwamna ke yi za su iya kasance masa Karfen Kafa nan gaba?

A matsayinmu na masu hankali nun san Allah ya Kaddara iyaka wa’adin da Nuhu GiDaDo zai yi ke nan a matsayin mataimakin gwamnan jihar Bauchi. A Kashin kansa ne ya yi wannan murabus Din, kuma kundin tsarin mulkin Kasa ya ba shi damar yin hakan, sannan kuma ya bayyana cewar ya yi hakan ne domin ‘yanta zuciyarsa daga wasu abubuwa. Amma mu a gwamnatance kafin jiya muna da masaniyar yana hutu ne, domin ya nemi hutun mako uku domin tafiya kula da lafiyarsa, don haka ajiye aikinsa a Kashin kansa haKKinsa ne ba za ka hana shi ba.

 

Me za ka bayyana kan cewar ya ga wasu matsaloli ne a cikin gwamnatin ya sa ya fice wanda kuma bai kamata daman ya jero su a daidai wannan lokacin ba?

Ni dai na sani Nuhu GiDaDo mutum ne dattijo, mutun ne wanda ba ya tsayawa Boye abin da ke ransa, inda akwai wani abu a ransa zai bayyana. Domin mu a Kashin kanmu abin da mutum ya faDa da shi muke aiki.

 

An ce gwamnatin ba ta tafiya da shi wajen gudanar da mulki ne ta maishe shi saniyar ware?

Amma a Dan sanina, ita gwamnati a lokacin da aka fara tafiyar nan, Nuhu GiDaDo ya samu dama daidai gwargwado, a shekara ta 2016 ya zama shi ne Aminirul Hajji. kwamitin farko da aka kafa a gwamnatin jihar Bauchi shi ne kwamitin sake fasalta harkar ilimi wanda gwamnan ya naDa Nuhu GiDaDo a matsayin shugaba, kuma shawarorin da suka bayar a wannan kwamitin har yanzu da su ake aiki a fannin ilimi wanda ya sa ma’aikatar ilimi ta kasance ita ce ke amsar kaso ma fi tsoka na kasafin kowace shekara. Sannan kuma babu wani Bangaren da aka sakar masa mara kamar ilimi a lokacin da mataimakin gwamna yake kwamishinan ma’aikatar. Bayan wannan gwamnan bayan rantsar da shi an tambaye shi mene ne zai fi maida hankali a kai ya ce ilimi. Bisa wannan dalilin ne ya Dauko ma fi kusa da shi wato mataimakinsa a wancan lokacin ya miKa masa amanar wajen, bayan nan a jihar nan ne aka zo aka bai wa Nuhu GiDaDo kwamishinan ma’aikatan ayyuka da sauransu. Don haka maganar bai samun dama a wannan gwamnatin bai ma taso ba.

 

Idan muka dubi tarihi ba Nuhu GiDaDo ba ne kawai ya yi murabus a wannan gwamnatin, wasu ma sun yi, ba ka ganin wasu za su ce gwamnatin ku Din nan akwai matsala kamar yadda ku kuke ta KoKarin rufewa?

A’a, ai duk wanda ya ajiye muKaminsa ya ajiye ne a bisa Kashin kansa wanda kuma ‘yancinsa ne wanda tsarin mulki ya ba shi. Abin da nake so ku gane da a ce gwamna ne yake cire su to nan ne matsalar take, kuma irin wannan matsalar ce ma aka samu a baya, ka duba tarihin jihar Bauchi dukkanin mataimakin gwamnan da aka cire, tsige shi aka yi, walau ta hanun majalisa ko ta wata hanyar ta daban. Sannan kuma dukkanin kwamishinoni da masu bayar da shawara da suka rasa kujerunsu a gwamnatocin baya cire su aka yi, amma a wannan gwamnatin su a Kashin kansu ne, kuma shi gwamna bai taBa faDa da su ba.

 

Kana ga har yanzu da sauran waDanda ba su gamsu da tafiyar gwamnan ba daga cikin waDanda suke muKarrabansa?

Ita siyasa kana yi dukka ne ko kuma ba ka yi, biyayya a siyasa ana yinta Dari bisa Dari ne, ko kuma ba ka biyayya. WaDannan kalmomi biyu da na faDa maka, idan ka ga mutum yana sassarfa to akwai yiyuwar yana da wani tunani bayan tunanin da muke da shi na cewar APC a jihar Bauchi a KarKashin jagorancin Muhammad Abdullahi Abubakar, don haka duk wanda bai gamsu a zuciyarsa ba, to ka ga babu abin da za ka faDa masa, illa dai ka ce masa Allah ya sa haka shi ne ma fi alheri a gare mu gaba Daya.

Irin wannan abin da yake faruwa, yana daidai da irin abin da iyayenmu ke faDa ne, duk matar da ta nemi kashe aurenta babu abin da waliyai za su yi domin su daidaita wannan zamantakewar auren matuKar matar nan ta yi niyyar ficewa to wallahi sai ta tafi, wannan kawai shi ne zaman lafiyarka. Amma mu Alhamudullahi duk waDanda suka tafi za ka samu sun kasa kasau a filin siyasar jihar Bauchi. Shi Nuhu GiDaDo na sa ya sha bamban da na sauran domin shi a Kashin kansa ne ya ajiye domin yana son ya ‘yanta zuciyarsa bisa Kashin kansa, saBanin sauran, ka ga ya kira gwamna wansa ya kuma kira gwamna jagoransa, bilhasali ma mu makusantan gwamnan jihar mun sani da kansa ne ya Dauki muKamin majidaDin gwamnan jihar Bauchi ka ga hakan na nuni da kyakkyawar fahimta da ke tsakaninsu, amma tunda siyasa ce kowa yana da Kididdigarsa.

 

Yanzu me za ku ce misa tun da ya ajiye muku muKaminku?

Allah ya zaBar masa abin da ya fi masa alheri, muna kuma fatan a kowane lokaci zai ci gaba da bai wa gwamnatinmu haDin kai domin samun nasarar gudanar da kyawawan ayyuka. Maganar 2019 ba ta hanun kowane daga cikinmu, daga waDanda suka bari da kuma jagororinmu  dukka wannan batun na zaBen 2019 na hanun Allah ne.

 

Wasu na ganin kamar mataimakin gwamnan nan ya yi murabus ne domin zai fito neman takarar gwamna a 2019?

Mu dai za mu duba kalamansa da kuma takardar da ya ba mu, don haka za mu tsaya a daidai yadda ya ce, kuma ya ce ya ajiye ne a Kashin kansa, shi Dan jihar Bauchi ne za mu jira mu ga ta inda zai fito. Mu yanzu muna KoKarin faDaDa haDin kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar APC kuma kanmu a haDe yake. A zaBen 2019 gwamna mai ci ne zai samu nasara, kamar yadda ya ci a 2015 da yardarm Allah .

 

Idan Nuhu GiDaDo ya fito neman gwamnan a 2019 ba zai kasance muku Karfen Kafa ba?

To ni ina da ilimin gaibu ne? kuma in zai fito ai na ce maka mu bari ya furta da bakinsa, idan ya furta a lokacin ne za ka gane Allah na tare da gwamna a lokacin ne za ka gane jiga-jigan APC suna tare da gwamna.

 
Advertisement

labarai