Connect with us

Madubin Rayuwa

Na Cika Burina A Nijeriya, In Ji Matashi Dan Kasar Sin Liao Jianfeng

Published

on

“Lokacin da na fara aiki a wannan kamfani, na ji an ce ‘za a yi farin cikin tafiya kasar waje a karon farko, a karo na biyu kuwa za a ji dan bakin ciki, kana a karo na uku ya dogara da aikin da mutum zai yi’. Idan na yi alkawarin cewa ‘zan yi aiki a Afrika har shekaru 10’, ba wanda zai yarda, amma yanzu na har tsawon shekaru 13 ina aiki a Afrika, shekaru 10 daga cikinsu a Nijeriya na yi, don haka burina ya cika.”
Wannan matashi mai suna Liao Jianfeng, an haife shi ne a birnin Meishan na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin wuri mai kayatarwa da ni’ima. Ya kammala karatunsa a jami’ar koyon ilmin sufuri ta kudu maso yammacin kasar Sin a shekarar 2005, daga wancan lokaci zuwa yau, ya shafe shekaru 13 yana aiki a nahiyar Afrika, ya taba aiki a matsayin mai kula da manyan ayyuka guda 7, kuma ya gana da shugabannin kasashen Afrika 5, wadanda suka ziyarci ayyuka da ya jagoranta. Liao Jianfeng ya ce, matasan dake aiki a kamfanin CCECC na da wani burin da suke cimmawa a Afrika, wato samun gindin zama a nahiyar Afrika duk da cewa akwai nisa wasu wahalhalu da kadaici da za su fuskanta.
Liao wanda ya fara aiki da karamin matsayi na injiniya a Afrika, yana kuma mayar da hankali kan aikinsa da ma sauke nauyin dake wuyansa, har ma bai iya komawa kasar Sin a lokacin bikin bazara ba, domin baiwa sauran abokan aikinsa damar saduwa da iyalansu, Liao ya yi tunani cewa,
“Ranar 18 ga watan Oktoba na shekarar 2008, shi ne karon farko da na je Nijeriya. Ina tsammani zan fuskanci mawuyacin halin. A shekaru 4 da rabi da na yi aiki a Nijeriya, na yi kokarin kara ilmina da shiga ayyuka da dama don habaka fasaha da kara kwarewata, ta wannan hanya na fara fahimtar da ma kaunar Nijeriya.”
An ce, “Sannu sannu kwana nesa”, kokarin da Liao Jianfeng ya yi ya biya shi, a karshen shekarar 2012, kamfanin CCECC ya yi nasarar samun aikin gina wasu manyan gine-gine a filayen jiragen sama guda 6 a Nijeriya da darajarsu ta kai dala milyan 800. Kuma Liao Jianfeng shi ne ya kula da aikin gini da kamfaninsa ya gudanar a filin jiragen sama na garin Enugu. Bikin bude babban aikin ya samu halartar tsohon shugaban Nijeriya na wancan lokaci Goodluck Jonathan, da kuma shugabannin jihohin kasar 5 da ’yan majalisu 13.
Liao Jianfeng yana mayar da hankali sosai kan aikinsa a Nijeriya, amma kuma ya shiga wani mawuyacin hali sakamakon wani hadarin mota da ya gamu da shi a kan hanyarsa ta zuwa wurin aiki, inda ya samu munanan raunuka, har ma likita ya ce hadarin ya shafi lakarsa. Saboda ganin irin wannan halin da yake ciki, abokansa suka ba shi shawarar komawa gida, amma Liao Jianfeng ya yanke shawarar ci gaban da aikinsa a Nijeriya, ya ce, “Da ma ba wanda ya yi tunani cewa, zai yi aiki a kasashen waje, yanzu kasar Sin na karawa matasa kwarin gwiwar zuwa kasashen ketare don dukufa kan aiki tare da kare mutunci da cika burinsu na rayuwa. Na warke sosai saboda jiyya mai kyau da na samu, matakin da ya sa na yanke shawarar ci gaba da aikina a Nijeriya.”
A shekarar 2015, ya cika shekaru 10 da zuwa Nijeriya. A watan Mayu na wannan shekara, an nada Liao a matsayin manaja na 9 mai kula da aikin jirgin kasan dake zirga-zirga a ciki da kewayen birnin Abuja, kuma darajar kudin wannan aiki ya kai dala miliyan 823. A cikin wa’adin aikinsa na watanni 18, ya kammala wasu muhimman ayyukan da suka hada da shimfida hanyar jirgin da hada hanyoyin jirgin waje guda. Liao Jianfeng ya ce, a shekaru 10 da na yi ina aiki a Nijeriya ko wace rana ina magana da ’yan Nijeriya, kuma sun yaba da ingancin ayyukan da kamfanonin kasar Sin ke gudanarwa da ma kwazon Sinawa na gudanar da wadannan ayyuka.
Babban injiniyan dake kula da wannan aiki na Nijeriya Tony Agbakoba, ya ce yana kaunar wannan aiki sosai, kuma a duk lokacin da ya yi magana kan wannan aiki ba zai manta da Liao Jianfeng da kamfanin CCECC ba, ya ce, “Jacques Liao mutum ne mai kirki, babu shinge tsakaninmu a duk lokacin da muke son yin magana da shi, kullum muna shafe sa’o’i da dama muna tattaunawa kan batun kimiyya da fasaha don tabbatar da ingancin aiki da yadda za a aiwatar da wannan aiki nan gaba. Wannan aiki akwai wuya sosai, saboda Abuja na da duwatsu da dama, hakan ya sa da farko muka damu sosai kan ingancin aikin CCECC, amma na girgiza kwarai da ganin yadda Sinawa suke gudanar da aikin. Musamman ma lokacin da na je birnin Beijing, na ga yadda Sinawa suke dukufa kan aikinsu, kuma suna mai da hankali sosai kan ingancin aiki. Wallahi, na ji dadi sosai domin aiki da wannan babban aiki, wanda ya gina hanyar jirgi irinsa na farko a yammacin Afrika. Ko shakka babu, ba zai sake gamuwa da irin wannan dama ba a zaman rayuwata. Kuma ina amincewa da CCECC, ina son in kara hada kai da wannan kamfani.”
An fara wannan babban aiki ne a ran 28 ga watan Mayu na shekarar 2009, saboda da karancin kudi, an dakatar da aikin. Injiniya Anthony Agwaniru ya tuna cewa, lokacin da dukkanin ma’aikata sun bacin rai saboda karancin kudi, gwamnatin kasar Sin ta ba mu taimako, ya ce, “Watan Agusta na shekarar 2012, bisa taimakon CCECC, bankin shige da fice na kasar Sin ya ba mu rancen kudi, matakin da ya farfado da wannan aiki, abin da ya inganta dangantakar abota tsakanin Nijeriya da Sin.”
Ran 12 ga watan Yuli na shekarar 2018, aka fara yin amfani da wannan layin dogo, bikin kaddamar da layin ya samu halartar shugaba Muhammadu Buhari. A matsayin layin dogo irinsa na farko da aka shimfida a yammacin Afrika, wannan ya kasance wani babban ci gaban da aka samu tun bayan taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika. Antony ya ce, layin dogon na da muhimmanci sosai ga mazauna wurin da kuma bunkasuwar tattalin arzikin Abuja, babban birnin Nijeriya. Layin dogon zai magance matsalar cunkoson zirga-zirga a Abuja da samar da tsaro da inganta jin dadin zaman rayuwa. Kuma zai kara mu’ammala tsakanin biranen dake kewayen Abuja, ciki hadda Kubwa, da kuma samar da guraben aikin yi ga mazauna. Dadin dadawa, ya samarwa kamfanonin kanana da matsakaita damamakin bude kofa ga waje, matakin da ya kara kudaden shiga na babban birnin Abuja. Antony na kaunar wannan aiki kwarai da gaske, kuma yana da imani sosai kan zumuncin Sin da Nijeriya. Ya ce, “Ina godiya sosai kan matakin da CCECC ya dauka na ba da muhimmanci kan kimiyya da ingancin aiki, ma’aikatansa na dukufa kan ayyukansu kwarai, suna yi iyakacin kokarin bayyana mana zumunci da mutunta bambancin dake tsakaninmu, a ganina suna kasance tamkar wata gada ta sada zumuci tsakanin kasashen biyu.
Ayyukan da CCECC ke gudanarwa na da inganci sosai kuma suke cike da fasahohi da kimiyya, abin da ya amfana mana saoai. Manajoji da ma’aikatansu na nuna mana dankon zumunci, har ma sun horar da ma’aikantanmu, ta yadda za mu gudanar da wadannan ayyuka nan gaba. Ina godiya sosai ga CCECC.”
Game da wannan babban aiki mai muhimmanci da ya taba kula da shi, Liao Jianfeng ya yi farin ciki da alfahari sosai a kai. Ya ce, na taka sa’a sosai domin shiga wannan aiki, matakin da ya bayyana amincewa da kamfaninmu ya yi da ni, na kuma bayyana kwarewata sosai a aikin. Ganin yadda aikin da ya gudana ya kara inganta dangantakar Sin da Nijeriya, ya yi farin ciki sosai, ya ce, “Da farko dai, burni na shi ne kammala wannan aiki yadda ya kamata cikin inganci. Saboda ganin mutuncin da ma’aikatan CCECC ke nunawa a cikin wadannan ayyuka, abokanmu na Afrika sun fahimci na’aunin kasar Sin na zamani da ingancin ayyukan kasar Sin. Burina ya cika a Afrika, kuma rayuwata na kara inganta a Nijeriya, Wannan ya sa burina a Afrika da kuma Nijeriya ya cika.” (Marubuciya: Amina Xu, ma’aikaciyar sashen Hausa na CRI)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: