Dubban jama’ar a Jihar Ribas sun taru a gaban gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal domin tarbar Gwamna Siminalayi Fubara.
Magoya baya daga ƙungiyoyi daban-daban suna ta rawa, da murna don nuna farin ciki da dawowar gwamnan.
- Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku
- Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka
Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu a daren ranar Laraba ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a jihar, wanda hakan yq sa aka dawo da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu, da ’yan majalisar dokokin jihar kan kujerunsu.
A ranar 18 ga watan Maris, 2025 Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas, tare da dakatar da gwamnatin jihar na tsawon watanni shida saboda rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fubara da tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike.
Rikicin ya jawo rabuwar kai a majalisar dokokin jihar a 2023, rikice-rikice kan sahihancin ’yan majalisa, zarge-zargen lalata bututun mai, da kuma ƙorafi cewa gwamnati ba ta aiki yadda ya kamata.
A lokacin dokar ta-ɓaci, Tinubu ya naɗa tsohon Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin wanda zai yi mulki na rikon ƙwarya.
A jawabin bankwana da ya yi da safiyar ranar Alhamis, Ibas ya roƙi ’yan siyasa a jihar su ci gaba da kiyaye zaman lafiya da haɗin kai da gwamnatinsa ta samar a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp