Rikicin jam’iyyar PDP ya ƙara ɗaukar sabon babi a ranar Asabar yayin da ɓangarori biyu na jam’iyyar suka dakatar da juna.
Wani ɓangare karkashin jagorancin sakataren jam’iyyar da aka dakatar, Sanata Samuel Anyanwu, ya sanar da dakatar da muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Umar Damagum, da wasu manyan jami’an jam’iyyar guda biyar.
- Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
- Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar
Anyanwu ya ce sun ɗauki wannan mataki ne saboda zargin rashin ƙwarewa, almundahana da rashin mutunta hukuncin kotu.
Ya naɗa mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa ta Tsakiya, Mohammed Abdulrahman, a matsayin sabon muƙaddashin shugaban jam’iyyar.
Sauran waɗanda aka dakatar sun haɗa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba; mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu, Taofeek Arapaja; sakataren kuɗi na ƙasa, Daniel Woyenguikoro; jagoran matasan jam’iyyar, Sulaiman Kadade; da mataimakin sakataren jam’iyyar na ƙasa, Setonji Koshoedo.
Wannan mataki ne awanni kaɗan bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da Anyanwu da wasu mutane uku, lamarin da ya ƙara ta’azzaea rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar PDP.














