A ranar 10 ga watan nan ne aka rufe bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE karo na 8, CIIE ya kasance bikin baje kolin daya tilo da aka mai da shigo da kayayyaki a matsayin babban takensa a duk fadin duniya, kuma muhimmin dandali ne da kasar Sin ke amfani da shi wajen inganta aikin bude kofa ga waje. Kana a matsayinsa na muhimmin matakin da kasar Sin ta dauka domin habaka bude kofa, CIIE ya zama muhimmiyar tagar da ake duba yadda kasar Sin ta canja daga mai bin sauran kasashe zuwa mai ba da jagora a fannin bude kofa.
Yadda kasar Sin ta ci gaba da habaka aikin bude kofa mai inganci ga sassan waje, tare da kara bude kofa ga waje cikin himma da kwazo, ya dace da halin kasuwannin kasashen duniya, tare da biyan bukatun al’umma na neman ci gaba da jin dadin zaman rayuwa, kana hakan ya samar da tabbaci ga kasashen duniya wajen karfafa harkokin bude kofa ga waje.
Kokarin da kasar Sin ta yi a fannin kara bude kofa ga waje ya samar da wata babbar kasuwa. Kafin bude bikin CIIE na wannan karo, kasar Sin ta kaddamar da jerin aikace-aikace bisa taken “Bude babbar kasuwa don shigowa da kayayyaki zuwa kasar Sin”, inda jama’ar kasar Sin suke duba hajoji daga kasashen ketare kai tsaye. A sa’i daya kuma, bude kofa ya ba da taimakon hada harkoki na zamani, ta yadda ake gaggauta aikin yin kirkire-kirkire a fannonin kimiyya da fasaha.
Bugu da kari, abu mafi muhimmanci shi ne, kasar Sin ta ba da jagoranci ga kasashen duniya ta fuskar kara bude kofa ga waje. Ta hanyar shigowa da kayayyaki da fitar da kayayyaki, kasar Sin ta ba da gudummawar bunkasa tattalin arzikin duniya, da kara yawan kayayyakin da kasashen duniya suke fitarwa, tare da ba da taimako ga kasashe masu tasowa wajen kyautata harkokin masana’antu. A sa’i daya kuma, kasar Sin ta ba da taimako wajen shigar da mambobin WTO su 130 cikin yarjejeniyar samar da sauki a ayyukan zuba jari domin neman ci gaba, ta yadda kowa zai cimma moriyar sakamakon dunkulewar duniya cikin adalci. (Mai Fassara: Maryam Yang)














