ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

by Sadiq
8 hours ago
Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya tayar da ƙura bayan wallafa rubutu a shafinsa na sada zumunta kan cewar Amurka za ta ɗauki matakin soji a kan Nijeriya idan ba a daina kisan Kiristoci.

Waɗannan kalamai nasa sun tayar da hankalin jama’a, inda ma’aikatar tsaron Amurka ta fara nazarin wasu matakai don yiwuwar kai wa Nijeriya hari.

Masana Sun Ƙaryata Iƙirarin

Amma masana tsaro, lauyoyi, da masana diflomasoyi a Nijeriya da ƙasashen waje sun ce wannan magana tasa ba komai ba ce illa barazana da kuma siyasa, kuma ba zai iya ɗaukar kowane mataki a kan Nijeriya ba.

ADVERTISEMENT

Masana a Nijeriya sun yi watsi da ikirarin Trump da hujjojin da ya dogara da su. Bulama Bukarti, lauya kuma mai nazarin matsalar tsaro, ya ce batun “kisan Kiristoci” ba gaskiya ba ne amma iƙirarin na iya rura wutar ƙiyayya tsakanin addinai.

Ya bayyana cewa matsalar tsaro a Nijeriya ba ta addini ɗaya ba ce, domin ‘yan ta’adda suna kashe Musulmi da Kirista baki ɗaya.

LABARAI MASU NASABA

Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa

Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna

“Dukkanin bayanan da ake da su sun nuna cewa babu wani kisan gillar da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya… Wannan labarin ƙarya ne da ƙungiyoyi suka ƙirƙira, wanda Shugaba Trump ke ƙoƙarin yaɗawa.

“Wannan magana za ta iya ƙara tayar da hankali a Nijeriya… ‘Yan ta’adda suna kai hare-hare a kasuwanni, coci-coci, da masallatai, kuma suna kashe kowa ba tare da bambance tsakanin Musulmi da Kirista ba,” in ji Bukarti yayin wata hira da gidan talabijin na Al-Jazeera.

Masana da dama sun yi gargaɗin cewa irin wannan kalamai daga shugabanni na iya haddasa tashin hankali a ƙasar.

Martanin Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta kuma mayar da martani ta hanyar ƙaryata batun cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya.

Ministan harkokin wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar, ya ce kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bai wa kowa damar yin addininsa cikin ‘yanci, don haka babu wani dalili da zai sa a ce gwamnati tana goyon bayan addini ɗaya.

Ya kuma ce Nijeriya na maraba da duk wani taimako da zai ƙara wa jami’an tsaronta ƙarfi wajen yaƙi da ta’addanci, amma cikin mutunta ƙasar.

Matakin Doka

A matakin doka kuwa, babu wata hanya da Amurka za ta iya kai wa Nijeriya hari kai-tsaye. Dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya sun hana kowace ƙasa kai hari sai da izinin Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

Haka kuma, dokar Amurka ta ‘War Powers Act’ na buƙatar shugaban ƙasa ya sanar da majalisa cikin awa 48 idan zai tura sojoji ƙasar waje, kuma ya buƙaci amincewar majalisa idan za a tsawaita zaman sojojin.

Wannan na nufin cewa babu wata doka da za ta bai wa Trump damar kai hari kai-tsaye a Nijeriya.

A ɓangaren matakin soji liwa, hakan ma ba abu ne mai sauƙi ba. Nijeriya tana da yawan jama’a sama da miliyan 220, tana da faɗin ƙasa da ke da wahalar sarrafawa, kuma rikice-rikicen da ake fuskanta a ƙasar sun samo asali ne daga ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da na masu aikata laifuka. Saboda haka, duk wani yunƙuri daga Amurka zai fi dacewa ya taƙaita ga bayar da horo, bayanan sirri, da tallafi wa sojojin Nujeriya, ba kai sojoji ƙasar ba.

Masana harkokin tsaro sun yi gargaɗin cewa irin wannan yunƙuri na iya haifar da tsadar abinci, asarar rayuka, da tashin hankali a ƙasar.

A yanzu dai, abin da zai iya yiwuwa shi ne amfani da hanyoyin diflomasiyya da takunkumi, maimakon yaƙi. Majalisar Dokoki ta Amurka na tattaunawa kan yiwuwar sanya wa mutanen da ke taimaka wa rikice-rikice a Nijeriya takunkumi, yayin da ECOWAS da sauran ƙasashen Afrika ke ƙaryata batun “yi wa Kiristoci kisan kiyashi”.

Masana a Nijeriya na jaddada cewa mafita game da lamarin shi ne haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa da tsare-tsaren tsaro masu mutunta ikon ƙasar.

A gefe guda wasu na ganin ana so a yi amfani da bambacin addini ko siyasa domin samun damar yi wa Nijeriya kutse don samu damar wawushe mata albarkatun ƙasa kamar man fetur, ma’adanai da sauransu.

Wani lauya masanin harkokin tsaro mai suna Barista El-Zubair na ganin cewa akwai wasu ɓoyayyun dalilai da ya sa Trump ya fara waɗannan maganganu.

“Idan ya ce zai ɗauki matakin soji a kan Nijeriya, ta ina zai fara?

Nijeriya tana da girma da faɗi, kuma ga tarin al’umma, don haka wasu dalilai ne kawai suka saka yake waɗancan kalamai, amma batun ana kashe Kiristoci ba gaskiya ba ne, kawai yana son fakewa da shi ne don cimma wata manufa tasa.”

A taƙaice, dokokin ƙasa da ƙasa, ƙalubalen dabaru, da ra’ayoyin masana sun tabbatar da cewa kalaman Trump tsagwaron barazana ce ta siyasa, kuma ba gaske ba ce domin babu wata hujja da ta nuna ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa
Manyan Labarai

Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa

November 12, 2025
Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna
Manyan Labarai

Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna

November 12, 2025
Coas
Manyan Labarai

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

November 11, 2025
Next Post
Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna

Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa

November 12, 2025
‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina

November 12, 2025
Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

November 12, 2025
Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa

Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa

November 12, 2025
Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna

Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna

November 12, 2025
Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

November 12, 2025
Coas

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

November 11, 2025
Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

November 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.