Rundunar ‘Yansandan Jihar Katsina ta sanar da kama mutane sama da 200 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a faɗin jihar a cikin watan Oktoba, 2025.
Mai magana da yawun rundunar, Sadiq Abubakar ne, ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar.
- Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro
- Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal
A cewar rundunar, an kama waɗanda ake zargin ne bisa laifuka sama da 120 da suka shafi fashi da makami, kisan kai, fyaɗe, fataucin miyagun ƙwayoyi, da garkuwa da mutane.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai 18 da ake zargi da fashi da makami, 28 da kisan kai, biyar da yunƙurin kisan kai, 20 da fyaɗe, da kuma 28 da mallakar miyagun ƙwayoyi.
Ya bayyana cewa an miƙa mutane 97 zuwa kotu, yayin da 22 ake ci gaba da bincike a kansu.
Ya ƙara da cewa rundunar ta samu nasarar ceto mutane 47 da aka yi garkuwa da su da kuma mutane 39 da aka ceto daga hannun masu safarar mutane, inda aka miƙa su ga iyalansu.
Kayan da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargi sun haɗa da bindiga AK-47 guda ɗaya, bindiga ta gida guda ɗaya, alburusai 183, motoci uku, babur mai ƙafa uku da keke napep ɗaya, da kuma dabbobi sama da 200 na sata.
Haka kuma, ‘yansanda sun ƙwato tarin miyagun ƙwayoyi irin su Fentalin, Exol, Tramadol, da wiwi, tare da wayar wutar lantarki.
Abubakar ya sake tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙari wajen tabbatar da tsaro, inda ya ce, “Duk da waɗannan nasarori, har yanzu akwai aiki da yawa a gabanmu. Mun ƙuduri aniyar ƙara ƙoƙari.”
Ya gode wa Sufeton ‘Yansanda na Ƙasa, Kayode Egbetokun, da Gwamnatin Jihar Katsina bisa goyon bayansu, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai da za su taimaka wajen hana aikata laifuka.














