Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa tare da shugabancin rundunar soji za su kare kowane jami’i da ke bakin aikinsa bisa doka.
Badaru ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida a ma’aikatar tsaro kan bikin tunawa da Sojojin Nijeriya na shekarar 2026, wanda aka gudanar a Cibiyar Tsaron Ƙasa (National Defence College), Abuja, a ranar Laraba.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa
- Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa
Kalamansa na zuwa ne bayan rikicin da ya ɓarke a bainar jama’a tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da wani jami’in rundunar sojan ruwa, Laftanar A. M. Yerima, kan wani fili da ke Abuja da ake zargin mallakar tsohon Shugaban Rundunar Sojan Ruwa, Vice Admiral Zubairu Gambo (mai ritaya) me.
Badaru ya ce rundunar soji ba za ta hukunta Laftanar Yerima ko wani jami’i da ke aikinsa bisa doka ba.
Ya ce: “A Ma’aikatar Tsaro, da ma rundunonin sojoji gaba ɗaya, za mu ci gaba da kare jami’anmu da ke aikin doka.
“Muna bincike wannan lamari, kuma muna tabbatar da cewa duk jami’in da yake aikinsa bisa doka, za a kare shi. Ba za mu bari wani abu ya same shi (Yerima) ba matuƙar yana aikinsa yadda ya kamata kuma yana yin aikinsa sosai.”














