Mataimakin wakilin dindindin na Sin a MDD Sun Lei, ya gabatar da jawabi yayin taron kwamitin sulhu game da batun Sudan ta Kudu da aka gudanar jiya Talata, inda ya yi kira da a inganta mika mulki cikin kwanciyar hankali a Sudan ta Kudu.
Sun Lei ya ce, Sin ta bukaci dukkan bangarorin kasa da kasa da su mayar da hankali kan yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, kana su dakatar da ayyukan da ka iya haifar da tashe-tashen hankula, musamman ma a hana amfani da karfin tuwo da kuma guje wa karuwar rikice-rikice.
Sun Lei ya kara da cewa, kasar Sin ta yi imanin cewa, mabudin warware matsalolin kasashen Afirka yana hannun Afirka. Duk wata mafita ya kamata ta kare ikon mulki kan Sudan ta Kudu da shugabancinta, tare da mutunta batutuwan da kasar ta damu da su.
Bugu da kari, Sun Lei ya bayyana cewa Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su kara ba da tallafi don daidaita tattalin arziki da rayuwar jama’ar kasar, da kyautata walwalar jama’arta, da kuma tallafawa Sudan ta Kudu wajen daukar hanyar samun ci gaba mai ’yanci da dorewa. (Safiyah Ma)














