A shekaru fiye da 20 da suka gabata, birnin Wenzhou dake lardin Zhejiang na kasar Sin ya yi suna domin samar da takalma, kuma kayayyakin da ya samar sun samu karbuwa a duniya domin suna da araha. Amma ma’aikatan kamfanonin samar da takalma sun yi aiki har na tsawon awoyi 14 a kowace rana, inda yawan takalman da aka samar a shekara daya ya kai miliyan 100, amma ribar kowane takalma biyu ba ta wuce Yuan biyu kacal ba, kana ba su da inganci, har ma mutanen Turai suna wa takalman shagube da sunan takalman yini daya.
Batun ya sa kaimi ga Xi Jinping wanda ya yi aiki a gwamnatin lardin Zhejiang da ya tsai da kudurin canja burin kamfanonin daga samar da kaya cikin sauri zuwa kyautata ingancin kayan.
A halin yanzu, kamfanonin samar da takalma na birnin Wenzhou suna amfani da fasahohin zamani na 3D wajen samar da takalman musamman, ribar takalma biyu ta karu zuwa Yuan 200, wannan ya shaida cewa, inganci ya fi daraja a kan yawa. Wannan ne misali na raya tattalin arzikin Sin mai inganci. Kasar Sin ta gudanar da matakai uku wajen samun ci gaba mai inganci da canja zaman rayuwar jama’a. Na farko shi ne yin kirkire-kikrire, na biyu shi ne canja tsarin samar da kaya don kiyaye muhalli, na uku shi ne bude kofa ga kasashen waje da more fasahohi a tsakanin juna. (Zainab Zhang)














